Kamar Yadda Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA-ya habarta cewa, an gudanar da taron kolin kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO tare da halartar Hujjatul Islam Wal Muslimeen shugaban kasar Iran Dr. Sayyid Ibrahim Ra'isi. Kasar Turkmenistan ce ta karbi bakuncin taron ECO karo na 15. Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Turkiyya, Pakistan, Afganistan, Turkmenistan, Kyrgyzstan, Uzbekistan, Kazakhstan, Tajikistan da Jamhuriyar Azarbaijan su ne kasashe 10 na kungiyar ECO.

30 Nuwamba 2021 - 12:01