An kashe fararen hula da dama a harin da 'yan Taliban suka kai a maboyar 'yan ta'addar ISIS a Kandahar.

17 Nuwamba 2021 - 15:40

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- ya bada labarin cewa jami'an kungiyar Taliban sun sanar da fara kai farmaki kan maboyar 'yan ta'addar ISIS a kudancin kasar Afganistan.
Wannan farmakin na sojan Taliban ya zo ne bayan hare-haren zubar da jini da kungiyar ISIS ta kai a makonnin da suka gabata.

Dakarun Taliban sun lalata wata maboyar ISIS a Kusa da Asibitin Sindakhan/Sidal da ke gundumar Kandahar ta hudu, inda suka kashe 'yan ISIL uku, kamar yadda mataimakin kakakin Taliban Inamullah Samangani ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya rubuta cewa an kuma kashe fararen hula biyu a yayin farmakin. Wasu kafafen yada labarai na cikin gida sun kuma bayar da rahoton wani artabu tsakanin dakarun Taliban da 'yan kungiyar ISIS a kudancin Afghanistan.

Abdul Ghaffar Mohammadi, babban jami'in 'yan sanda na kungiyar Taliban a lardin Kandahar, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, an fara kai farmakin da suke kai wa reshen Khorasan na kungiyar ISIS a gundumomi hudu na lardin da tsakar daren ranar Litinin din da ta gabata, kuma har zuwa safiyar yau.

Mohammad ya ce: "Ya zuwa yanzu, an kashe mayakan ISIL hudu tare da kame wasu mambobin kungiyar guda goma." Daya daga cikinsu ya tarwatsa kansa a wani gida.

Wani jami'in leken asirin Taliban da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an kashe fararen hula uku a harin.

Kafofin yada labaran kasar Afganistan sun ruwaito a safiyar litinin cewa, da alama an samu fashewar wani abu a yammacin birnin Kabul wanda ya yi sanadin jikkatar mutane da dama.

Tun bayan da kungiyar Taliban ta karbi mulki, reshen Khorasan na ISIL na kai hare-hare a lardunan Nangarhar, Kunduz, Kandahar da Kabul.

342/