Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) - ABNA ya bayyana, an gudanar da zaman makokin Muharram 1443 (2021 Miladiyya) a Argentina, kamar yadda aka yi a duk sassan duniya. A wannan shekara, saboda Matsalar takunkumin Korona, an gudanar da wannan taron makokin ne a kafar yanar gizo inda ya samu jawabin Hujjatul Islam Wal Muslimeen"Abdullah Sarija" bi sa daukar nauyin "Cibiyar Musulunci da Masallacin Tawhid" a Buenos Aires, babban birnin Argentina. An watsa taron kai tsaye a kafafen sada zumunta a sararin yanar gizo. Hakanan ana iya samun taskar tarihin wannan taron a tashar Tawhid Center akan dandalin ta na bidiyo na "YouTube".

8 Satumba 2021 - 14:14