Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Jaridar Isra'ila Maariv ta bayyana wani yanayi na damuwa mai zurfi da ya dami manyan 'yan siyasa da tsaro a Isra'ila, saboda tsoron yuwuwar ƙulla yarjejeniyoyi cikin sauri ta ɓangaren Trump da abokan gaba na yankin.
Jaridar ta jaddada cewa babban tsoro yana cikin maimaita yanayin "ƙulla yarjejeniyar Amurka da Houthi a yaƙin da ya gabata kwatsam" a duk wani rikici mai yuwuwa. Isra'ilawa na fargabar cewa Trump zai iya cimma wata yarjejeniya ta ba zata, wacce za ta ba shi damar ayyana "nasara ta kashin kansa" ya kuma ja da baya daga kololuwar hadafinsa, wanda zai bar Isra'ila ita kadai ta sha kashi tare da fuskantar matsalolin tsaro.
Jaridar ta bayyana cewa halin Trump a baya tare da Yemen ya zama abin koyi mai ban tsoro ga rundunar ƴan mamaya. Bayan ya yi amfani da barazanar da ya saba yi da kuma hare-haren bama-bamai na soja na yau da kullun, ya yi gaggawar kammala "yarjejeniyar" da ta dakatar da yaƙi da sojojin Amurka kawai, ba tare da ya tabbatar da wani alƙawari daga 'yan Houthi ba na dakatar da harba makamai masu linzami a Isra'ila ba.
Sakamakon ya nuna cewa barazanar Yemen ta ci gaba, kuma sun ci gaba da kai hare-harensu "a duk lokacin da suka gadama ta yadda suke so," wanda ya sa Isra'ila ta bayyana su a matsayin " mummunan mafarkin da ka iya faruwa a yanzu" wanda ba za a iya hasashen shi ko hana fatuwarsa ta hanyar shiga tsakani na Amurka.
Maariv ta nuna cewa abin da manyan Isra'ila ke tsoro yanzu shi ne cewa Washington za ta yi nasarar samo sassauci daga Tehran game da batun nukiliya (fiye da abin da Obama ya samu), amma a madadin mayar da hankali kan manyan makamai masu linzami na Iran da ayyukan wakilanta a yankin.
Wannan yanayin yana nufin cewa yarjejeniyar da Amurka da Iran za su iya cimmawa na iya tabbatar da tsaron muradun Amurka, amma zai bar Isra'ila "gaba da gaba" da makamai masu linzami na Yemen da Iran ba tare da kariya daga siyasa ko soja na duniya ba don tabbatar da dakatar da waɗannan hare-haren.
Binciken Ibrananci ya kammala da cewa dogaro gaba ɗaya kan "yarjejeniyar Trump" na iya zama farar asara. Manufar da shugaban Amurka ke bi ita ce cimma daidaito wanda ke aiki a cikin gida na Amurka da kuma kimarsa a matsayin "mai samar da zaman lafiya," yayin da Isra'ila ta kasance mafi rauni ga makamai masu linzami da ke ketare iyakoki da kuma shiga tsarin tsaron sama. Wannan yana buƙatar mamaye yankin ya sake tantance lissafinsa, yana barin duk wani ruɗani na cikakken kariya ta Amurka.
Your Comment