Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Majalisar sadarwa da Yada sakonnin Musulunci ta sanar da yin Allah wadai da matakin haramci da Tarayyar Turai ta dauka kan Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci tana mai cewa: Al'ummar Iran tana tare da masu kare tsaronta da 'yancin kanta, kuma irin wadannan yunkuri ba wai kawai ba za su kawo cikas ga kudurin kasa ba, kai har ma za su kara hadin kai, taka tsantsan, da kuma kudurin hadin kan Iraniyawa ne.
Suma a nasu bangaren Sojojin Iran, a cikin wata sanarwa da suka mayar da martani ga yunkurin da EU ta yi kan rundunar kare juyin juya hali:
Sun tabbatar da cewa: Mun tsayawa kyam tare da rundunar kare juyin juya hali wajen fuskantar ta'addanci da magoya bayanta.
Waɗanda ke ikirarin yaki da ta'addanci sune magoya bayan tsarin 'yan ta'adda Sahyuniyawa. Kasashen Turai suna cudanye da jinin Iraniyawa 17,000 a hannunsu sakamakon kungiyoyin 'yan ta'adda da suka turo zuwa kasar.
Turawa sun sanya babbar ƙungiyar yaƙi da ta'addanci a yankin da kuma duniya a cikin jerin ƙungiyoyin ta'addanci da su suka ƙirƙira, suna biyan muradun Amurka da tsarin Sahyuniyawa.
Your Comment