10 Janairu 2026 - 20:20
Source: Almanar
Hanzala Ta Bayyana Jami'an Mossad 600, Wanda Suke Haifar Da Hargitsi A Iran

A cewar takardun da kungiyar ta wallafa, jerin sunayen sun hada da sunayen wasu sanannun mutane, tare da tabbatar da gazawar ƙungiyar mamaya wajen haifar da rashin zaman lafiya a cikin kasar.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kungiyar masu kutse ta "Handala" a kwanan baya ta wallafa hotunan wani babban jami'in Mossad mai suna "Mehradad Rahimi", lura da alakarsa da 'yan tarzoma a Iran. “Hotunan Handala, wadanda aka dauka kai tsaye daga wajen gidan Rahimi, yayin da suke lura da bin diddiginsa, sun nuna karara cewa babu wani motsinsa da ya rasa daga idonun Hanzala,”.

Sanarwar ta kara da cewa "har ma sun yi kutse a wayarsa mai kariya, lamarin da ya kai ga gano duk mutanen da ke da alaka da hanyoyin tarzoma na Iran da kuma sanya su cikin sa ido." 

Kungiyar ta ce, "Wadannan hujjojin ba wai kawai suna raunana 'yancin kai da kwarewar Rahimi ba ce, har ma sun sake nuna girman tasirin basirar Hanzala sun tabbatar da cewa hatta manyan jami'an Mossad ba su da kariya daga kutsen Handala," suna mai jaddada cewa dukkan wakilai. da manyan Jami'an Mossad yanzu an san su sosai kuma mun bayyana su".

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha