Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Shafin yanar gizo na Cairo 24 ya rubuta: "A cikin wannan jawabin, shugaban Majalisar Mulkin Sudan, yana mai nuni da halin da ake ciki a jihar Darfur, ya tabbatar wa mutane cewa sojoji sun fito fili don kare 'yancinsu da tsaronsu, kuma yaƙin da ake yi a yanzu yaƙi ne na kare mutunci da wanzuwar ƙasa. Ya jaddada cewa za a kafa gwamnatin Sudan ta gaba bisa ga "Tarayyar dukkan yan ƙasa tare da wakilci na dukkan bangarorin jama'a".
Abdul Fattah Al-Burhan, shugaban Majalisar Mulkin Sudan, ya jaddada a cikin sanarwar da aka fitar bayan ci gaban da kasar ta samu kwanan nan cewa babu wani yunƙuri na raba ƙasar da zai yi nasara kuma ƙasar Sudan tana da ikon fuskantar duk wani tawaye da barazana na cikin gida, kamar yadda ta gagari mulkin mallaka.
Your Comment