28 Satumba 2024 - 19:58
Sakon Ta'aziyyar Jagoran Juyin Juya halin Musulunci Bisa Shahadar Sayyid Hasan: Hare-Haren Ɓangaren Gwagwarmaya Za Su Afkawa Gajiyayye Kuma Lalataccen Jikin Gwamnatin Sahyoniyawa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a cikin sakonsa na ta'aziyyar shahadar babban mujahid kuma ma'abucin gwagwarmaya, Hujjatul-Islam Sayyid Hasan Nasrullah ya taya murna tare da mika gaisuwar juyayin shahadar shugaban kungiyar Hizbullah da babu irinsa zuwa ga kungiyar gwagwarmaya da al'ummar musulmi.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul Bait As - ABNA - ya habarta cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike da sakon ta'aziyyar shahadar babban mujahid kuma jagoran gwagwarmaya Hujjatul-Islam Wal Muslimin Sayyid Hasan Nasrallah a lokacin da yake taya murna da ta'aziyyar shahadar jagoran Hizbullah na musamman ga dukkanin fagagen gwagwarmaya da al'ummar musulmi da kuma bayyana zaman makoki na kwanaki biyar a kasar ya jaddada cewa: tushen da ya kafa a kasar Labanon da har ya bawa sauran cibiyoyin iko, tare da rashin Sayyid Aziz, bawai kawai gwagwarmaya ba zata gushe ba ne a'a sai dai ma da albarkacin jininsa da sauran shahidan wannan waki'a, karfinta zai kasance mai yawa da kai hare-hare na gaba a kan gajiyayya kuma rugujajjiyar jiki mulkin Sahayoniya da zai masa dukan murkushewa.


Nassin sakon jagoran juyin shine kamar haka;


Da sunan Allah, Mai rahama Mai Jinkai 


بسم اللّه الرحمن الرحیم

انا للّه و انا الیه راجعون


Ya ku al'ummar Iran

Al'ummar Musulunci masu girma

Babban Mujahid wanda yake rike da tuta a wannan yanki, malami mai kyawawan halaye da sanin Addini, kuma shugaban siyasa haziki, Sayyid Hasan Nasrallah Allah ya jikansa da rahama, ya samu shahada a waki'ar daren jiya a kasar Lebanon kuma ya tashi zuwa masarauta daukaka Sayyid madaukaki na gwagwarmaya ya samu ladan Jihadi na shekaru da dama da suka gabata don neman yardar Allah da wahalhalunsa a lokacin gwagwarmaya mai tsarki. Ya yi shahada ne a lokacin da yake gudanar da shirye-shiryen kare mutanen da ba su da matsuguni na yankunan da ke wajen birnin Beirut da gidajensu da aka ruguza da kuma aka daidaita su, kamar yadda ya shafe shekaru da dama yana tsare-tsare da shirye-shirye na gwagwarmayar kare al’ummar Palastinu da ake zalunta waɗanda aka kwace garuruwa da kauyuka tare da ruguza gidaje da 'yan uwansu da akai masu kisan kare dangi. Tabbas Falalar samun shahada kaitsaye itace zata kasance rabonsu bayan dukan Wannan gwagwarmayar.

Duniyar Musulunci, manyan mutane masu mutumci da girma Sannan da kungiyar gwagwarmaya sun yi hasarar fitaccen mai rike da tuta, kuma Hizbullah ta rasa shugaba mara misaltuwa, amma albarkar Jihadin da ya kwashe shekaru da dama yana yi ba zai taba rasa shi ba. Tushen da ya assasa a kasar Labanon, da har ya samarwa sauran cibiyoyin gwagwarmaya karfi, ba zai gushe ko ai yayi hasararsa kadai, a'a, sai dai zai sami karfi albarkacin jininsa da sauran shahidan wannan waki'a. Hare-haren yan gwagwarmaya da suke kaiwa yi kan tsohuwar gwamnatin Sahayoniya da ta lalace kuma take kan Hanyar rugujewa da ikon Allah zai kara ƙarfi irin dukan Kawo wuka. Mummunar dabi'ar gwamnatin Sahayoniya ba ta yi nasara ba a cikin wannan lamari.

Jagoran gwagwarmaya ba kawai iya mutum ba ne, tafarki ne kuma makaranta, kuma haka za a ci gaba. Jinin shahidi Sayyid Abbas Musawi bai watsu a kasa hakanan ba, haka nan jinin shahidan Sayyid Hasan ba zai kwarara a kasa hakanan ba.

Zuwa ga mai girma matar Sayyid madaukaki wacce kuma ta ba da danta Sayyid Hadi a gabanta bisa tafarkin Allah, da ‘ya’yanta da iyalan shahidan wannan lamari, ga kowane dan Hizbullah, da masoyansu da jama'a da manyan mahukuntaan kasar Labanon, da kuma dukkanin fagagen gwagwarmaya, ina taya daukacin al'ummar musulmi ta'aziyyar shahadar Sayyid Nasrallah da sahabbansa da suka yi shahada, tare da bayyana zaman makoki na kwanaki biyar na al'umma a kasar Iran. Ina rokon Allah ya tashe da waliyansa.

Wassalamu ala Ibadihis Saliheen 

والسلام علی عبادالله الصالحین

Sayyid Ali Khamenei


28/09/2024