Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Da suke gabatar da jawabai a wajen taron kolin dandalin bunkasa ayyukan gona na Afrika (AGRF) na shekarar 2021, wanda ke gudana a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, shugabannin sun ce, akwai bukatar a sauya salon ayyukan noma domin bunakasa samar da abinci, da tabbatar da inganta samar da sinadarai masu gina jiki da bunkasa hanyoyin samun kudaden shigar mazauna karkara yayin da nahiyar ke fadi-tashin neman farfadowa daga mummunan tasirin da annobar COVID-19 ta haifar.
Kasar Kenya ce ke karbar bakuncin taron kolin na AGRF na 2021 daga ranakun 7 zuwa 10 ga watan Satumba, mai taken “Hanyoyin farfadowa da karfafa tsarin samar da abinci".
342/