Kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (a.s.) - ABNA - ya habarta cewa, Wadi al-Salam makabarta ce da ke birnin Najaf Ashraf kusa da haramin Imam Ali (a.s.). Hadisan da suka zo a cikin madogaran hadisi game da falalar wannan makabarta sun nuna irin matsayin da take da shi. A cikin wannan makabarta akwai kaburburan Annabi Hudu da Saleh, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, daga cikin annabawan Ubangiji da aka ambata a cikin Alkur'ani, da kuma kaburburan malamai da muminai da dama.

17 Satumba 2022 - 05:16