Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA 24
Laraba

22 Disamba 2021

15:58:31
1211349

Shekh Dakta Ridha Zaari’i Khurmizy: Matukar Addinin Musulunci Yana Raye To Lalle Shekh Zakzaky Yana Raye

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo rahoton cewa, A yau Laraba 22/12/2021 bayan sallah Azuhur An gudanar da taron tunawa da waki'ar Zaria wacce ta faru shekaru shida da suja wuce a cikin Jami'ar Ahlul Bayt International dake Tehran inda taron ya samu halartar mutane da dama daga cikin malamai da daliban Jami'ar taron ya samu halartar Babban Malamin Jami'ar Doktor Hujjatul Islam Wal Muslimeen Shekh Ridha Zari'i Khurmizy Malami mai koyarwa a tsangayar Tarihin Musulunci na Jami'ar inda ya gudanar da bayani mai ratsa jiki ga mahalarta taron Babban Malamin ya tabo janibobi da yawa na rayuwa da ayyukan Shekh Ibrahim Zakzaky da irin kokarin da yayi yake kuma cikin yi a harkar yada Addinini Musulunci da Mazhabar Ahlul Bayt As Malamin ya tabo janibin yanda wannan waki'a ta faru da kuma irin sadaukarwar da yan uwa Musulmi su kayi na bada rayuwa kansu musamman Shekh Zakzaky da mai dakinsa inda yayi bayanin irin yadda suka rasa 'ya'yansu guda shida a waki'o'u guds biyu tare da rasa mabiya da suka haura sama da dubu bisa farmaki da hukuma take kai masu ta hanyar anfani da jami'an tsaron ksa ba tare da wani dalili ba.

Malamin yayi bayani da dama akan waki'ar data faru a 12-14 ga disambar shekara ta 2015 inda jimi’an tsaro tsawon wadannan raneku suka farwa mabiya Ahlul Bayt da kisa ba ji ba gani inda suka kai hari Husainiyah Baqiyatullah inda Shekh din ke gudanar da karatutta da kuma gidan sa dake unguwar Gyallesu cikin birnin Zaria da kuma Makabarta ta Darur Rahama inda suka kashe kowa a Husainiyya tare da rusheta sannan gidan Shekh din ma sun kashe kowa sannan suka kama malamin tare da mai dakinsa suka tafi dasu bayan sun harbe su harbi na kisa. Inda suka tsare sun a tsawon shekuru shida ba tare da laifin komai ba ko wani dalili.

Malamin ya ci gaba da bayani inda Yace dangane da Shekh Zakzaky : Matukar Addinin Musulunci Yana Raye To Lalle Shekh Zakzaky Yana Raye
Inda kuma ya kwatanta Malama Zenatudden Ibrahim da cewa: har yanzu Masu Kama Da Sayyidah Ummul Baniin Basu Kare Ba Malama Ta Kasance Ummul Banin Din Zamanin Mu...

Akarshe Anyi Addua ga daukacin wadanda sukai Shahada da nema masu rahamar Allah Ta'ala ga kuma wadanda suka wanzu da samun sabati da kariya daga makiya.

Rahoto: Shafiu Kabiru