Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (A.S) wanda ya samu gayyata daga musulmin Brazil domin halartar taro mai taken "Musulunci Addinin Rayuwa Da Tattaunawa Ne" ya isa zuwa wannan kasa, a gefen wannan tafiya, inda ya ziyarci sassa daban-daban na gine-ginen al'adun masallacin Sayyidina Muhammad Rasulullah (SAW) da ke birnin Sao Paulo na kasar Brazil.

4 Mayu 2024 - 18:25