Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: “Jose Antonio Protzo”, babban limamin birnin Curitiba na kasar Brazil, ya gana da Ayatullah “Riza Ramazani”, Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya Ayatullah Ramadani wanda yayi tafiya zuwa wannan kasa bayan samun gayyata daga Musulman Brazil don halartar taron kasa da kasa mai taken “Musulunci; Addini Ne Na Tattaunawa Da Rayuwa".

4 Mayu 2024 - 17:49