Yayin da miliyoyin al'ummar kasar Yemen ke fadawa cikin yaki da fatara da yunwa, labari game da yiwuwar dawo da tallafin jin kai na MDD ya bude wata kofar fatan alheri a zukatan al'ummar kasar.
Amir Saeed Irawani, jakada kuma wakilin din din din na jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana cikakken goyon bayan kasar Iran ga al'ummar Palastinu, wajen tabbatar da hakkinsu na cin gashin kansu, ya kuma yi kira da a gaggauta tsagaita bude wuta ba tare da wani sharadi ba, da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa, da cikakken kasancewar Palasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya.