Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ma'aikatar Harkokin Waje ta Afirka ta Kudu ta umarci babban jami'in hulda na Isra'ila, babban jami'in diflomasiyya da ke zaune a Pretoria, da ya bar ƙasar cikin awanni 72.
Dangantaka tsakanin gwamnatin Afirka ta Kudu da gwamnatin Isra'ila ta tabarbare tun lokacin da Pretoria ta shigar da ƙara a Kotun Duniya a ƙarshen 2023, tana zarginta da aikata kisan kare dangi a Gaza.
Ma'aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Juma'a cewa ta sanar da gwamnatin Isra'ila game da qudirin da ta yanke na ayyana Ariel Seidemann, babban jami'in hulda da jama'a a ofishin jakadancin Isra'ila, a matsayin wanda ba a amince da shi ba. Ma'aikatar ta ƙara da cewa qudirin "ya biyo bayan jerin keta ƙa'idodi da ayyuka na diflomasiyya da ba za a yarda da su ba, waɗanda ke nuna keta haƙƙin mallaka na Afirka ta Kudu kai tsaye"
Ta ƙara da cewa, "Waɗannan keta dokokin sun haɗa da yawan amfani da dandamalin sada zumunta na Isra'ila don yin batanci ga Shugaba Cyril Ramaphosa, da kuma kin sanar da aka yiwa ma'aikatar game da ziyarar da manyan jami'an Isra'ila suka kai".
Ma'aikatar Harkokin Waje ta ce, "Dole ne Sideman ya bar Afirka ta Kudu cikin awanni 72," kuma ta yi kira ga gwamnatin Isra'ila da ta tabbatar da cewa jami'an diflomasiyyarta a nan gaba "su nuna girmamawa ga Afirka ta Kudu".
Yaƙin Gaza ya yi tasiri a Afirka ta Kudu, wadda take gida ga mafi yawan al'ummar Yahudawa a yankin kudu da hamadar Sahara kuma ana ɗaukarta ɗaya daga cikin manyan masu goyon bayan manufofin Falasɗinawa.
A watan Nuwamba, Ministan Harkokin Wajen Afirka ta Kudu Ronald Lamola ya yi Allah wadai da "shirin korar Falasɗinawa daga Gaza, Yammacin Kogin Jordan, da yankunan da ke kewaye" bayan da wasu Falasɗinawa 150 suka isa filin jirgin saman Johannesburg ba tare da tambarin fita daga Isra'ila a cikin fasfo ɗinsu ba. Jirgin, wanda ke ɗauke da maza, mata, da yara, ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Eilat zuwa Nairobi, inda fasinjojin suka hau wani jirgin zuwa Johannesburg.
Ma'aikatar ta ƙara da cewa ƙarin dalilin dakatarwar shine "sanarwar da aka ki yinta da gangan kuma ba ta cika ba" game da ziyarar da jami'an Isra'ila suka kai Afirka ta Kudu, wanda ta ɗauka a matsayin keta dokokin girmama juna da kuma halayen diflomasiyya tsakanin ƙasashe.
Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da Afirka ta Kudu ke ci gaba da goyon bayan manufar Falasɗinu da kuma ci gaba da kin amincewa da manufofin mamayar haramtacciyar ƙasar Isra'ila, a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinu a wasu ƙasashen Afirka da Larabawa.
Your Comment