Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ofishin Rundunar Hashdush Sha’abi da ke lardin Basra ya sanar a jiya, Juma'a, cewa tawagar tallafin kayan aiki ta shi daga Basra zuwa kan iyakar Iraki da Siriya.
A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Baratha, Birgediya Janar Fadel al-Basiri, darektan ofishin Rundunar Hashdush Sha’abi da ke Basra, ya sanar a cikin wata sanarwa cewa wannan ayarin kayan aiki a zahiri wani ayarin jama'a ne da aka aika don tallafawa da taimakawa jami'an tsaro da Rundunar Hashdush Sha’abi da ke zaune a kan iyakar Iraki da Siriya.
Ya kara da cewa: Aikewa da wannan ayarin yana nuna ruhin hadin kan kasa da kuma tsayawa tare da sojojin da ke kare tsaro da kwanciyar hankali na Iraki.
..........
Your Comment