Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara :
Laraba

8 Mayu 2024

20:58:35
1457246

Bidiyon Yadda Babban Bishop Na Brazil Yi Mamakin Game Da Jin Labarin Bayyanar Imamul Mahd As

Wani takaitaccen bayani daga taron "Jose Antonio Protezo" Archbishop na Curitiba na kasar Brazil, tare da Ayatullah Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlul-Baiti (a.s) ta duniya da kuma yadda babban limamin cocin ya nuna mamaki da ban sha'awa game da labarin bayyanar Imamul Mahdi As. Ayatullah Ramadani kamar yadda muka sani ya yi tafiya zuwa wannan kasa ne bisa gayyatar da musulmin Brazil suka yi masa domin halartar taron kasa da kasa mai taken: Musulunci Addinin Tattauanawa Ne Da Rayuwa.

Madogara :
Laraba

8 Mayu 2024

19:14:34
1457219

Babban Bishop Na Curitiba, Brazil Ya Gana Da Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Bait (AS) + Bidiyo

Jose Antonio Protezo, Archbishop na Curitiba na kasar Brazil, ya gana da Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlul-Baiti ta duniya.

Madogara :
Laraba

8 Mayu 2024

12:11:03
1457098

Iyalan ISIS 'Yan Amurka, Kanada, Holland da Finland Sun Fara Komawa Gida

Wasu Amurkawa 11, da ‘yan Canada shida, da ‘yan kasar Holland hudu da kuma dan kasar Finland daya da ke cikin kungiyar ta’addanci ta ISIS sun koma kasashensu.

Madogara :
Laraba

8 Mayu 2024

11:55:21
1457095

Gaza | Ofishin Yada Labaran Gwamnatin Gaza: An Kara Gano Kabarin Bai Ɗaya A Rukunin Asibitin Ash-Shifa Da Ke Gaza + Bidiyo

Gaza | Ofishin Yada Labaran Gwamnatin Gaza: An Kara Gano Kabarin Bai Ɗaya A Rukunin Asibitin Ash-Shifa Da Ke Gaza

Madogara :
Laraba

8 Mayu 2024

08:25:17
1457069

Ayatullah Ramezani: Muna Bukatar Hadin Kan Mabiya Ahlul Baiti (AS) Wajen Ba Da Taimakon Jin Kai Ga Gaza.

Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul Baiti (AS) ya bayyana cewa: Idan muka yi tadabburi a kan koyarwar addini, addini ba ya kawo rudani, sai dai yana kawar da rudani ne. Addini yana buɗe ƙulli a cikin rayuwar ɗan adam kuma yana ba da aminci ga ruhin ɗan adam kuma yana ba da wani nau'i na nauyin da ya hau kai a cikin haɓaka sadarwa ga ɗan adam.

Madogara :
Laraba

8 Mayu 2024

06:26:28
1457040

Manjo Janar Rashid: Idan IRGC Da Sojoji Sukai Aiki Tare, Za’a Gama Da Isra'ila Ta Ƙare Da Aiki Ɗaya Ba Sai Anyi Karo Na Biyu Ba.

“Jiragen Yakin Sojojin Amurka Da Na NATO 240 Ne Suka Taimaka Wa Isra'ila Wajen Kare Harin Ladabtarwa Da Iran Tai Akan Isra’ila. Gwamnatin Yahudawan Sahyoniya Ba Ta Ba Kuskuran Iya Nunawa Duniya Hotunan Illar Harin Na Iran Ba”.

Madogara :
Laraba

8 Mayu 2024

05:56:25
1457025

Bidiyo | Daliban Amurka Suna Yajin Cin Abinci Don Nuna Goyon Bayansu Ga Falasdinu

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Kamar yadda kafar yada labarai ta CNN ta ce, bayan harin murkushe su da kame dubu biyu daga cikinsu, sun jaddada cewa za su ci gaba da yajin aikin har sai an biya musu bukatunsu na ganin an daina kaiwa Falasdinawa hari ta sama da kasa.

Madogara :
Laraba

8 Mayu 2024

05:46:26
1457022

Masu Kare Hakkin Bil Adama Suna Cikin Taskun Bazarana

Sanatoci 12 na jam'iyyar Republican sun yi wa babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da iyalinsa barazana

Madogara :
Talata

7 Mayu 2024

20:10:48
1456951

Yadda Isra'ila Ta Kai Harin Bama-Bamai A Tantuna 'Yan Gudun Hijira A Rafah

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewaa: gwamnatin sahyoniyawan na ci gaba da ruwan hare-haren ta sama da kasa da nufin rusa Hamas a Rafah. Wanda wannan bidiyon yana dauke da harin da suka kai akan tantinan yan Gudun Hijira da ke birnin Rafah ba jimawa da hada rahotan nan. Wannan duka ya biyo bayan tattaunawar tsagaita wuta da take kan gudana da amincewar bangarorin guda biyu.

Madogara :
Talata

7 Mayu 2024

20:02:32
1456949

Bidiyon Yadda Tankokin Yakin Isra'ila Suka Shiga Mashigar Birnin Rafah

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: tankokin gwamnatin sahyoniyawan sun samu damar shiga tare da ke tara mashigar birnin Rafah domin gudanar da kai hare-haren ta kasa da nufin rusa Hamas. Wanda tun a ayu suka fara ruwan bama-bamai a wasu yankunan na birnin. Wannan duka ya biyo bayan tattaunawar tsagaita wuta da take kan gudana da amincewar bangarorin guda biyu.

Madogara :
Talata

7 Mayu 2024

19:34:13
1456948

A Taron Ganawa Da Malamai Masu Tabligi Da limaman Juma'a Na Indiya;

Ayatullah Ramezani: Ya kamata Limaman Juma'a Su Tsaya Tsayin Daka Wajen Yaƙi Da Bidi'o'i, Shubuhohi Da Sauka Daga Addini.

Babban sakataren Majalisar Ahlul Baiti (A.S) ya bayyana cewa: Limaman Juma a birnin da yake aiki ya kamata ya gina ma'aikata da horar da masana ta hanyar zakulo mutane masu nagarta da aiki da kuzari da gabatar musu da hukunce hukuncen addini.

Madogara :
Litinin

6 Mayu 2024

18:28:25
1456634

Labarai Cikin Hotuna Na Yadda Birnin Khan Yunus Ya Koma Bayan Janyewar Dakarun Yahudawan Sahyuniyawa

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: wadannan hotuna na nuni da irin barnar da dakarun yahudawan sahyuniya suka yi a garin Khan Yunus na zirin Gaza bayan hare-haren da suka kai ta sama da ta kasa wanda yanzu suka janye daga birnin inda suka bar birnin a rushe kakaf.

Madogara :
Litinin

6 Mayu 2024

18:20:19
1456633

Jiragen saman Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a yankuna 2 na Rafah.

"UNICEF" Tayi Gargadi Game Da Bala'in Harin Da Ke Gabatowa Ga Yara Falasdinawa 600,000 A "Rafah"

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadi game da wani sabon bala’i da ke shirin afkuwa kan yara sama da dubu 600 a wannan birni a yayin harin da ‘yan mamaya zasu kai kan birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza.

Madogara :
Litinin

6 Mayu 2024

18:00:25
1456630

Labarai Cikin Hotuna Na Yadda Falasdinawa Suke Yin Hijira Daga Gabashin Birnin Rafah Bayan Sanarwar Isra'ila Na Kai Hari

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya bayar da rahoton cewa: bayan sanarwar da sojojin yahudawan sahyoniyawan suka yi na kauracewa wasu unguwanni a gabashin Rafah da ke kudancin zirin Gaza, Palasdinawa mazauna wannan yanki sun fara ficewa daga yankin da wuraren su.

Madogara :
Litinin

6 Mayu 2024

11:09:46
1456507

Jaridar (Ra’ayi; Yaum) Ta Rubuta Cewa: Shin Netanyahu Zai Amince Da Sharuddan Gwagwarmaya Ko Kuwa Yakin Zai Ci Gaba?

Netanyahu Ya Yaudari Kowa Da Kowa / Ya Nace Akan Ci Gaba Da Yakin Kisan Kai

A wata makala da ta yi tsokaci kan tsarin tattaunawar tsagaita wuta a zirin Gaza, jaridar Larabci ta "Ra’ayul-Youm" ta rubuta cewa bayan an samu kyakkyawan yanayi kan aiwatar da wannan tattaunawa tsakanin Hamas da Tel Aviv, tare da shiga tsakani na Masar da Qatar, kuma alkawarin cimma matsaya ya yi kusa, domin ganin an kawo karshen yakin da ake yi a Gaza, sai ga lamarin ya gaza samun dorewa, kuma alamu masu ban tsoro sun nuna cewa har yanzu ba a kai ga gaci ba.

Madogara :
Lahadi

5 Mayu 2024

08:32:40
1456216

Rahoto Cikin Hatuna Na Gudanar Da Zaman Makokin Shahadar Imam Sadik (A.S.) A Lambun Shahidan Ali Bin Jafar (A.S.) Da Ke Birnin Kum.

Kamfanin dillancin labaran na kasa da kasa na Ahlul-Bait (A.S) ya kawo maku rahoton cewa: an gudanar da zaman juyayin shahadar Imam Jafar Sadik (a.s.) tare da jawabin "Hujjatul Islam Wal muslimiin "Mahdi Daneshmand" da kuma waken juyayi daga Hajji Syed Mahdi Mirdamad" a Gulzar Shahada Ali bin Jafar (a.s.) a birnin Qum. Hoto: Hadi Cheharghani

Madogara :
Lahadi

5 Mayu 2024

08:25:56
1456211

Rahoto Cikin Hatuna Na Gudanar Da Zaman Makokin Shahadar Imam Sadik (A.S.) A Husainiyar Imam Amirul Muminin (A.S.) A Birnin Isfahan.

Kamfanin dillancin labaran na kasa da kasa na Ahlul-Bait (A.S) ya kawo maku rahoton cewa: an gudanar da zaman makokin shahadar Imam Sadik (a.s.) a Husainiyar Imam Amirul Muminin (A.S.) Isfahan (a.s) in da ya samu halartar mutane daban-daban.

Madogara :
Asabar

4 Mayu 2024

19:12:23
1456092

Rahoto Cikin Hotuna Na Halartar Shugaban Majalisar Ahlul-Bait (AS) A Makarantar Hauzar Curitiba Kasar Brazil.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (A.S) wanda ya samu gayyata daga musulmin Brazil domin halartar taro mai taken "Musulunci Addinin Rayuwa Da Tattaunawa Ne" ya isa zuwa wannan kasa, a gefen wannan tafiya, inda ya halarci makarantar hauza ta Curitiba, Brazil, kuma ya ba da jawabi ga ɗaliban wannan makarantar hauza.

Madogara :
Asabar

4 Mayu 2024

19:06:08
1456091

Hoto: Hadi Cheharghani

Rahoto Cikin Hotuna Na Halartar Babban Shuagaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) A Masallacin Sayyidina Ali bin Abi Talib (AS) Da Ke Curitiba A Kasar Brazil.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (A.S) wanda ya samu gayyata daga musulmin Brazil domin halartar taro mai taken "Musulunci Addinin Rayuwa Da Tattaunawa Ne" ya isa zuwa wannan kasa, a gefen wannan tafiya, inda ya samu ziyarar masallacin Sayyidina Ali Abi Talib (AS) da ke birnin Curitiba na kasar Brazil, kuma ya yi jawabi ga gungun musulmi a wannan masallaci.

Madogara :
Asabar

4 Mayu 2024

18:25:23
1456088

Labarai Cikin Hotuna Na Ziyarar Da Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya Ya Kai Ginin Al'adu Na Masallacin Sayyidina Muhammad Rasulullah (AS) Da Ke Birnin Sao Paulo Kasar Brazil.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (A.S) wanda ya samu gayyata daga musulmin Brazil domin halartar taro mai taken "Musulunci Addinin Rayuwa Da Tattaunawa Ne" ya isa zuwa wannan kasa, a gefen wannan tafiya, inda ya ziyarci sassa daban-daban na gine-ginen al'adun masallacin Sayyidina Muhammad Rasulullah (SAW) da ke birnin Sao Paulo na kasar Brazil.