Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

8 Mayu 2024

19:14:34
1457219

Babban Bishop Na Curitiba, Brazil Ya Gana Da Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Bait (AS) + Bidiyo

Jose Antonio Protezo, Archbishop na Curitiba na kasar Brazil, ya gana da Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlul-Baiti ta duniya.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: "Jose Antonio Protzo", babban limamin coci a birnin Curitiba na kasar Brazil ya gana tare da Ayatullah "Riza Ramazani" babban sakataren majalisar ta Ahlul-Bait (AS) wanda ya gayyata daga Musulman Brazil don halartar taron kasa da kasa "Musulunci Addinin Tattaunawa Da Rayuwa Ne” ya samu damar isa wannan kasar.

A farkon wannan taro, Jose Antonio Protzo ya bayyana jin dadinsa a ganawarsa da Ayatullah Ramezani inda ya ce: Ina fatan in samu yin kyakkyawan hotu a farfajiyar masallatai mafi kyau na Iran.

Babban sakataren Majalisar Ahlul-baiti (A.S) ya ci gaba da yin ishara da sifofin Ubangiji inda ya ce: Allahn da aka gabatar a Musulunci, abin so ne kuma abin kauna, wanda kuma ya kamata a so; Shi ne Allahn dukkan kamala da dukkan kyawawan abubuwa kuma Allahn kyau da daukaka.

Ayatullah Ramezani ya bayyana cewa: Wajibi ne mu san nauyin da ke kanmu ga masu yin zalunci; Da farko dai mu kyamaci duk wani mulkin zalinci, kai ya ma zamo kuma mu fuskanci zalunci mu hana don kada a kara zaluntar mutane sama da haka domin ya zamo rahamar Ubangiji ta yadu.

Ya kara da cewa: Mun yi imani Annabi Isa (a.s) zai zo ya kasance tare da mai cetonmu domin ya cika adalci.

Bishop Protzo ya bayyana cewa: Akwai abubuwa da dama da Musulunci da Kiristanci suka hadu da juna. Littafin kare hakkin bil'adama yana da tushe mai zurfi a gare ni, amma ban yi tsammanin cewa shekaru 1200 da suka gabata, wadannan batutuwa sun fito ne daga addininku (Risalatul Hukuk ta Imam Sajjad As).

Babban Bishop na Curitiba ya ce: Muna bukatar mu yi bincike na tarihi don baayyana arzikin ma’ana na Musulunci.

A karshen wannan taro, babban sakataren Majalisar Ahlul-Baiti (a.s) ya gabatar da littafin Imam Sajjad (a.s) Risalatul Hukuk ga babban limamin birnin Curitiba na kasar Brazil tare da wani Allon zane da aka zana sunan Allah da Annabawa Ulul Azam ajikinsa, a matsayin alamar hadin kai tsakanin mabiya addinan Ubangiji.

Nan ba da dadewa ba za a buga cikakken rubutu da bidiyon wannan taro a kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA.