Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

6 Mayu 2024

11:09:46
1456507

Jaridar (Ra’ayi; Yaum) Ta Rubuta Cewa: Shin Netanyahu Zai Amince Da Sharuddan Gwagwarmaya Ko Kuwa Yakin Zai Ci Gaba?

Netanyahu Ya Yaudari Kowa Da Kowa / Ya Nace Akan Ci Gaba Da Yakin Kisan Kai

A wata makala da ta yi tsokaci kan tsarin tattaunawar tsagaita wuta a zirin Gaza, jaridar Larabci ta "Ra’ayul-Youm" ta rubuta cewa bayan an samu kyakkyawan yanayi kan aiwatar da wannan tattaunawa tsakanin Hamas da Tel Aviv, tare da shiga tsakani na Masar da Qatar, kuma alkawarin cimma matsaya ya yi kusa, domin ganin an kawo karshen yakin da ake yi a Gaza, sai ga lamarin ya gaza samun dorewa, kuma alamu masu ban tsoro sun nuna cewa har yanzu ba a kai ga gaci ba.

Wannan kafar yada labaran ta kara da cewa: Matsayin jami'an yahudawan sahyoniya da na kungiyar Hamas a cikin sa'o'i kadan da suka gabata suna jaddada cewa har yanzu yarjejeniyar ba ta cimma ruwa ba, sannan kuma akwai cikas da dama a hanyar tsagaita bude wuta a Gaza.

A cewar Ra’ayil Youm, duk da kokarin da Masar ke yi na samar da yanayi mai kyau a tattaunawar da kuma nasarar da aka samu, amma hakikanin gaskiyar da ke faruwa a cikin dakunan da aka rufe ta sha bamban da matsayin kafofin yada labarai nisan tazarar kasa da sama da kuma hakan na nuna nisa da ke akwai wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wutar da musayar fursunoni tsakanin Tel Aviv da Hamas.

Wannan kafar yada labarai ta ci gaba da cewa: "Mahmoud Mardawai" daya daga cikin shugabannin kungiyar Hamas ya jaddada bukatun Hamas na mayar da komawar gudun hijirar, da sake gina zirin Gaza da kuma janyewar 'yan mamaya gaba daya daga wannan yanki, shi kuma "Hussam Badran" mamba shi a ofishin siyasa na kungiyar Hamas ya kuma yi nuni da cewa, wannan yunkuri bai haifar da cikas ba a kan hanyar yin tattaunawar ana zargin Netanyahu da majalisar ministocinsa da kawo cikas wajen kokarin dakatar da shirin tattaunawar.

Ra’ayul Yaum ta kara da cewa: A sa'i daya kuma, kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyawan sun sanar da cewa, damar cimma matsaya a yayin shawarwarin tsagaita bude wuta a zirin Gaza da musayar fursunoni kadan ne, ko da yake kafofin watsa labaru na kasar Masar sun ba da rahoton samun ci gaba a tattaunawar. Har ila yau, wani jami'in yahudawan sahyuniya ya jaddada batun shigar sojojin gwamnatin kasar cikin Rafah, kuma Tel Aviv ba za ta mika wuya ba har zuwa karshen yakin.

Wannan kafar yada labarai ta harshen larabci ta rubuta cewa: Majiyar da ke da alaka da gwagwarmayar Palastinawa ta bayyana cikas da dama da ke akwai a kan hanyar yin tattaunawar, sakamakon adawar mamaya na tsagaita bude wuta na dindindin, yayin da Hamas ke adawa da yarjejeniyar da ba za ta kai ga tsagaita bude wuta ba. Netanyahu ya hana samun nasarar tattaunawar kuma bai damu da dawowar fursunonin sahyoniyawan ba da bukatunsu da kalubalen duniya ta hanyar ci gaba da yakin kisan gilla.

Ra’ayul Yaum ta kara da cewa: Kokarin da masu shiga tsakani na kasashen Qatar, Masar da Amurka suke yi na shawo kan bangarorin da su amince da tsagaita bude wuta da musayar fursunoni domin kawo karshen yakin Gaza, tare da barin hakan ya ci gaba wanda ya haifar da matsalar jin kai da lafiya da ba a taba ganin irinsa ba tare da samun sama da mutane 34,000 Shahidai da suka hada da yara da mata. Netanyahu ya yaudari kowa kuma Masar ta yi fushi da wannan salon. Shin Netanyahu zai amince da sharuddan gwagwarmaya ko kuwa yakin zai ci gaba?