Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Asabar

19 Oktoba 2019

11:59:12
988151

An Sake Bude Mashigar Khosravi Ga Masu Ziyarar Arba'in

Bayan rufe mashigar Khosravi na nan wasu kwanuka, kasar Iraki ta bude mashigar ga masu ziyarar Imam Husain (a.s) a wannan Litinin.

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya habarta cewa a wannan litinin jami’an tsaron kan iyakan kasar Iraki sun bude mashigar Khosravi, bayan da suka rufeta na wasu ‘yan kwanaki saboda dalilai na tsaro, wanda hakan zai baiwa masu ziyarar Arba’in na Imam Husain (a.s) damar shiga kasar ta mafi kusan hanya na zuwa birnin Karbala’i.

Mashigar Khosravi ita ce mashigar kasar Irakimafi kusa daga kasar Iranna zuwa biranan Bagdaza da Karbala’I da kazimin gami da Samira’a.

Wannan matsiga ta Khosravidake arewacin kasar Iran zuwa Birnin Bagdaza nada nisan kilomita 190, sannan kuma zuwa birnin Najab nada nisan kilomita 380, kamar yadda kuma ke da nisan kilomita 300 zuwa birnin Karbala’i.



/129