Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Pars Today
Asabar

10 Agusta 2019

08:29:55
967911

Najeriya: Falana Ya Yi Watsi Da Sharuddan Gwamnatin Jahar Kaduna

Femi Falana ya kakkausar suka game da sabbin sharudda da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar ka fin a fita da jagoran yan uwa musulmi sheikh Ibrahim Elzkzki zuwa Asibiti a kasar Indiya.

(ABNA24.com) Femi Falana ya kakkausar suka game da sabbin sharudda da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar ka fin a fita da jagoran yan uwa musulmi sheikh Ibrahim Elzkzki zuwa Asibiti a kasar Indiya.

Rahotanni dake fitowa a Nigeria sun bayyana cewa fitaccen lauywan kuma dan ragin kare hakkin dan adama Nigeria ya caccaki gwamantin jihar Kaduna game da sabbin sharudan da ta bullo dasu kafin su amince a fita da jagoran yan uwa musulmi sheikh Ibrahim Elzakzaki da maidakinsa zuwa kasar Indiya domin nemanmagani kamar yadda kotun koli ta yanke hukumci, idai dai gwamnatinjihar Kaduna ta nuna damuwarta ne game da yiyuwar sheikh zakzaki ya nemi mafakar siyasa a kasar ta Indiya.

Daga cikin sharudda masu tsauri da gwamanan jihar Kaduna Mal Nasiru El’ Rufa’I ya gindaya akwai bukatar a samu wani fitaccen mutum ko kuma wani sarki mai daraja ta dayaa jihar Kaduna da zai tsaya musu, kafin a bari su fita zuwa kasar ta Indiya, saboda bata aminta da yanayin da zaa tafi da malam din zuwa Asibitin ba,

Daga karshe ya kara da cewa tun dahukumar liken asiri ta kasaDSSta da ke rike da Malama halin yanzu ta sanar da matsayinta a madadin gwamnatin tarayya na bin hukumacin da kotu ta yanke ya bukaci gwamnatin jihar Kaduna da ta janye batun duk wasu sharudda domin wani mataki na mena tsokana da ka iya dawo da hannun agogo baya.



/129