Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Talata

6 Agusta 2019

07:06:12
967297

Nageriya:SSS Tana Shirin Bin Umurnin Kotu Dangane Da Lafiyar El-Zagzaky

Hukumar jami’an tsaron farin kaya ta bada sanarwan cewa tana shirye-shiryen bin umurnin kotu dangane barin sheikh Ibrahim Zakzaky zuwa kasar India don jinya.

(ABNA24.com) Hukumar jami’an tsaron farin kaya ta bada sanarwan cewa tana shirye-shiryen bin umurnin kotu dangane barin sheikh Ibrahim Zakzaky zuwa kasar India don jinya.

Kamfaninin dillancin labaran NAN ya bayyana cewa a jiya litinin ce wata babban kotu a Kaduna ta bada belin shugaban Harka Islamiyya ta yan shi’a da matarsa malama Zinat don jinya a kasar Indiya tare da wasu sharruda.

Tun shekara ta 2015 ne dai ake tsare da sheikh Zakzaky bayan dirar mikiyan da jami’an tsaro suka yi masa da mabiyansa a gidansa dake unguwar gellesu a birnin Zari’a.

A halin yanzu dai albarusai da raunuka da suke cikin jikinsu ne suka galabaitar da su wanda ya zama tilas a fita da su zuwa kasashen wajen don jinya.

Kakakin hukumar ta DSS Peter Afunanya ya tabbatar da cewa sun karbi umurnin kotun kuma sun fara aiki don aiwatar da shi.







/129