Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Talata

30 Yuli 2019

06:21:21
965747

A mako mai zuwa ne kotu za ta yanke hukuncin bayar da belin Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaky

Kotun koli a jahar Kaduna wacce take shari’ar Malam Ibrahim El-Zakzaky, wacce ta yi zama a jiya Litinin, ta sake tsayar da ranar Litinin mai zuwa a matsayin lokacin da za ta yanke hukunci na karshe akan bayar da belin Shehun malamin da mai dakinsa malam Zinat.

(ABNA24.com) Kotun koli a jahar Kaduna wacce take shari’ar Malam Ibrahim El-Zakzaky, wacce ta yi zama a jiya Litinin, ta sake tsayar da ranar Litinin mai zuwa a matsayin lokacin da za ta yanke hukunci na karshe akan bayar da belin Shehun malamin da mai dakinsa malam Zinat.

Sake daga lokacin ci gaba da sauraron karar ya biyo bayan muhawarar da ta gudana ne a tsakanin lauya mai bayar da kariya ga shehun malami, Femi Falana, da kuma mai wakiltar gwamnati Dari Bayero.

Shi dai lauyan mai wakiltar gwamnati ya nuna adawa dad a belin Sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaky, yana mai cewa za a iya yi masa magani a cikin gida Najeriya ba sai an fitar da shi zuwa kasar waje ba.

Gabanin fara zaman shari’ar,an cika titunan birnin Kaduna da jami’an tsaro, tare da rufe muhimman tituna baki daya.



/129