Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Husa TV
Asabar

27 Yuli 2019

06:50:42
964701

​HRW Ta Bukaci A Saki ‘Yan Shi’a A Najeriya

Kungiyar Kare Hakkin ‘yan adam ta Human Rights Watch ta bukaci jami'an tsaron Najeriya da su daina yin amfani da karfi wanda ya wuce kima wajen tarwatsa masu zanga-zanga a Najeriya musamman ma amfani da karfin bindiga.

(ABNA24.com) A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta hannun babbar mai bincike na kungiyar, Anietie Ewang, ta ce dokokin Majalisar Dinkin Duniya dai sun ce 'jami'an tsaro za su iya yin amfani da "hanyoyin da ba na karfi ba da farko wajen warware takaddama kafin yin amfani da karfin", kuma a duk lokacin da yin amfani da bindiga ya zama wajibi to jami'an tsaron su yi amfani da karfin dai-dai kima yadda ba za su wuce gona da iri ba.

Kungiyar ta kara da cewa Majalisar ta Dinkin Duniya ta kuma ce "za a iya yin amfani da bindiga ne kawai idan rashin yin amfanin da ita zai janyo asarar rayuka.

Har ila yau kungiyar ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta gudanar da sahihin bincike kan hakikanin abin da ya faru a ranar 22 ga watan Yuli domin hukunta duk wadanda aka samu da laifi, sannan ta bukaci gwamnati da ta saki masu zanga-zangar da 'yan sanda suka kama ba bisa ka'ida ba, sannan kuma wadanda suka jikkata a cikinsu a kai su asibiti.

A ranar Litinin ne dai magoya bayan harkar Musulunci karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Elzakzaky suka gudanar jerin gwanon neman a sake shi, inda jami'an tsaro suka yi amfani da karfi da hakan ya hada da harbi da bindiga domin tarwatsa su, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar masu zanga-zanga 11 da dan sanda daya da kuma dan jarida guda.



/129