Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : tsk
Lahadi

29 Yuli 2018

14:16:54
903528

HADISAI AL-MAUDU'ATU ALATH THIQAAT ---- Sheikh Hamzah Muhammad Lawal

A karatun ranar juma'a, 20/7/2018, da Sheikh Hamzah Muhammad Lawal da ya gabatar a makarantarshi dake PRP U/Sanusi Kaduna yayi takaitaccen bayani dangane da hadisan da ake ce ma "Al-Maudu'atu Alath Thiqaat" a yayin da yake cigaba da bayanin hadisin Muslim da ire-irensa wayanda malaman Ahlus Sunnah suke amfani dasu suke tawili da taujihi da bata wasu hukunce hukunce wayanda Manzon Allah (saw) yayi a kan mutane a rayuwarsa ta risala.

Shehin Malamin yace wayannan mutanen da Manzon Allah (saw) ko ya tsine masu ko ya kore su ko ya dauki wani mataki a kansu sun rama. Bayan sallatar da wadancan hukunce hukuncen nashi Manzon Allah din, da farragar dasu daga MUHTAWA dinsu (su hukunce hukuncen da riwayoyin), to, sun dauki matakai a kan shi Manzon Allah din. Daga cikin matakan akwai ramawa a kan Manzon Allah din, da cin mutunci da zubar mashi da mutunci, kuma sun sanya wayannan a cikin littafai na hadisi da na tafsir da na sirah da na hukunce hukunce da sauransu.
Malamin ya ce:
 "Mun karanta maku hadisi guda daya a karshen darasin da ya wuce domin ilzam, wato domin lizimta masu. Muka ce ya za a ce kuce Manzon Allah (saaw)- a wurin bayani naqdiy da muke yi masu ko muka yi masu. Ya za a yi kuce Manzon Allah (saw) yana zagi ko ya fusata alhali kunce shedaninshi ya musulunta. Wannan riwayar da ire-irenta zamu kawo maku su da yawa. Suna daga cikin matakin ramako. Allah Yayi yawa da irin wayannan riwayoyin a cikin littafansu.
 "Sun ce wai wata rana Ummul Mu'uminina Aishah tayi fushi- ba wai dole ya zama haka ya faru ba. Mun sha fada maku hadisan da ake ce ma su "AL-MAUDU'ATU ALATH THIQAAT", wato hadisan da aka kirkira na karya sai a dora su a harsunan amintattu, sai a ce wane yace Manzon Allah ya yi.  Kai wanda kake kallo shine can karshen wane din wanda daga shi sai Annabin amma ba zaka tsaya ka yi bahasi a kan abinda ya hada ka kai yanzu da wannan wanen ba wanda yake jingine da Annabi (saaw). Bahsi na sanadi ba zaka yi ba balle kuma ka zo kayi bahsi na matani ka ga inda ya dace da Shari'a da hankali saboda ka aminta da Littafin da aka ce daga nan hadisin ya shigo.
 “AL-MAUDU’AT ALATH THIQAAT wata rana kila zamu yi bahasi a kan wayannan irin hadisan. Hadisan kad’an zamu kawo da shi wannan MAFHUM din na ALMAUDU’AT ALATH THIQAAT. Wani lokaci shi THIQAH din da gaske ya fadi abin kuma ba daidai bane. Wani lokaci LA, Miskin, ba shi ya fadi ba, an dora ne, an kirkiro ne sai aka dora a harshenshi aka ce shi yace, saboda an san ka aminta dashi. An san kana gasgata shi, an san kana girmama shi, an san amintacce ne a wurinka. Suma wayannan irin hadisan masha Allah, Allah Yayi yawa dasu, wayanda aka kirkire su aka dora su a kan Ath-Thiqaat. Sai su ce ka zagi sahabi su lullube su rufe.
 “Wata rana wai Ummul Mu’uminina Aishah ta fusata sai Manzon Allah (saw) yace mata; Me ya same ki? Shedaninki ne ya zo maki?- Ka ga akwai lokacin da shedaninta yake zo mata, kuma shi Annabin ne ya tambaye ta. Yace me ya faru? Hala shedan dinki ne ya zo maki? Sai tace; to, kai baka da shedanin ne? Subhanallah- Ka ga inda gaske ta fada haka, kad’an bata kyauta ba. Yanzu mu muna cewa ne bata ce ba an dora a kan harshenta. Duk da haka ba zamu tsira ba, kuma bamu muka yi riwayar ba, mu muna nakalto riwayar ne, ba tsira zamu yi ba, ta ko’ina ba zamu tsira ba amma duk da haka zamu fadi. Yanzu mu muna cewa ne an dora riwayar akan harshenta ne domin an tsallake ta a je ga manufa wadda itace a tabbatar da Annabi yana da shedan. Lura, wannan riwayar manufarta itace a tabbatar da Annabi (saw) yana da shedan, musulmi ko kafiri ba ishkal kowa yana da shedan, sai akai tawassali da Ummul Mu’uminina Aishah- haka muka ce mu an kirkire riwayar ne aka dora a harshen wani aka bi ta hanyarta domin a tabbatar da cewa Manzon Allah yana da shedan. To, koda ba haka bane, hakikatan ita ta fadi bamu karba ba, ba daidai bane. In muka ce bamu karba sai suce ya zagi Ummul Mu’uminin. Ba su gane abinda muke nufi ba. Bamu karba saboda Annabi (saw) ba zai yiwu a ce yana da shedani ba.
 “Wancan karan lokaci ya kure mana ne shi yasa. Ba da mai riwayar muke da matsala ba, ba da Ummul Mu’uminina muke da matsala ba, da cin mutuncin Annabi (saw) da jingina mashi shedan, da wannan muke da matsala. Daga yanzu mutane su dinga gane wannan. Bahsainmu ba bahsin Ummul Mu’uminina bane, lala Abadan. Mun fadi wannan a da. Ku dauki wannan uslubin. Bahsinmu ba bahsin Ummul Mu’uminina bane asasan. Abadan, ba ita ta dame mu a nan. A nan wurin ba ita bane maudu’u, ba ita bace maqsudah, Al-Maqsud shine Manzon Allah a ce yana da shedan. Kuma sai aka sa mata rashin adab. Yana fa mata fada ne a riwayar da su suka rawaito, ba riwayar mu bace. A wurinsu wannan riwayar ta inganta daga Muslim, ba a wurinmu ba. Wannan riwayar asasan ba riwayarmu bace, riwayar Muslim ce kuma a wurinsu ta inganta saboda ta afku a Muslim. Fada fa yake yi mata in kuka lura a riwayar. Ta fusata, yana ce mata ta kar kiyi fushi, fushin da aka ce shi yana yi saboda baya iya rike kanshi amma ga shi yana wa wani fada kada yayi fushi- kai akwai tanaqudaat a cikin wannan riwayar. (Sunce) shi fa yana fushi har ma ya fadawa Allah ba zan iya daina fushi ba, saboda haka duk lokacin da nayi fushi na zagi wani ka maida zagin ya zama qurba, amma gashi yana ce ma wani kar kayi fushi. Shi ba zai iya kasa fushi ba amma yanzu yana cema wani kar yayi fushi. SUBHANALLAH.
 “To, shike nan, a riwayarsu din yana kwabar ta a kan cewa shedaninki ya zo maki? Me ya kamata tayi? Ta tarbiyantu, ta karba, ta nemi gafarar Allah, ta nemi gafarar Manzonshi ko? Sai tace mashi; kai baka da shedan ne? Muslim yace Ummul Mu’uminina ta cewa Annabi baka da shedan ne? To, in suka gano abin ba daidai bane bai kamata su karbi abinda ta fadi ba a gefe daya a Hankalinsu da kwakwalwansu. Idan hankalinsu yace masu wannan bai kamata ya zama tasarrufin Ummul Mu’uminina ya zuwa ga Annabi ba a gefe daya. Sai a daya gefe kuma shi hankalin yace masu amma Muslim ne ya rawaito. To, sai ayi yaya kenan? Hankalin ko Muslim? Idan hankalinsu yace wannan ba zai yiwu ba bai kamata ba, wato bai kamata ba aqlan. To, sai addinantuwansu da addini da rikonsu da riwaya sai kuma wannan a gefe daya sai yace masu amma Muslim ne yace. To, sai kuma su cigaba su ce shi ko Muslim ma’asumi ne a aikace- ba mu ce a nazariyyance ba – duk abinda ya rawaito daidai ne ingantacce ne. To, saboda haka sai dole su nufi wata hanya ta uku, shine ta’awil. Sai suyi ta’awil sai suce wannan wani abu ne wanda ya shafi miji da matanshi, saboda haka kayi shiru. Yanzu sunan Annabi miji, sunan Aishah mata. Mata ta samu tayi wa mijinta irin wannan koda haka din ba daidai bane. Saboda haka wannan ta’awil din ya danne maka hankalinka ya tilastaka ka bi hadis. Ba mu muka rawaito riwayar ba.
 “To, shike nan sai tace to kai baka da shedan ne? Sai (Annabi) yace; ee, ina da mana, sosai ma ina da shedan- ka ga an zo an tashi daga kuskuren Ummul Mu’uminina ko? Yanzu kwata kwata an manta da maganar ta fusata, yanzu an komo Annabi- Amma na roki Allah sai ya taimake ni ya dora ni a kanshi, saboda haka sai ya musulunta- a wurinshi Kenan ya amshi shahada ko? Shedan din bamu san wane shedan ne a nan ba? Iblis ko Ifritu minal jinni ko wani nau’I na shedanu. Saboda shi dai Iblis bai musulunta ba. Wannan shedan ne na musamman na Annabi, (Shedan khas) ga Annabi, shine wannan wanda ya musulunta din. Wannan shedan din da ya musulunta ka tabbata ba shi bane Iblis, ko shine? Wannan shedan ne na musamman wanda duty dinshi a kan Annabi take. To, sai ya roki Allah sai Allah Ya taimake shi a kanshi sai ya musulunta, saboda haka bai umurta ta sai da alkhairi.
 “Ka ga shedaninshi shi yake umurtan shi. Shedanin Annabi shi yake wa Annabi umurni. Da ya musulunta din yanzu billahi alaik way a kamata y aba wani umurni Kenan? Tunda yanzu ya musulunta ya kamata ba ya dinga bin umurnin Annabi Kenan ba? To, sai yace bai umurta ta sai da alkhairi. To bamu sani ba in yana umurtanshi ne kawai da alkhairi, to, lokacin da yake so tsine ma wayannan wayanda bai cancanta din ba, ina wannan shedanin yake? Duka wannan ya kamata mutum ya amsa. A lokacin wannan shedanin baya nan? Koko shi shedanin ne ya umurce shi da ya tsine din kuma yace mashi tsinuwar alheri ce? Saboda a cikin wannan riwayar sun nuna cewa shedanin bai hana shi ba. Yana umurtanshi da alkhairi to kila kuma bai hana shi alkhairi ko? A muslim. To, wannan tana daga cikin riwayoyi wayanda suke suna da yawan gasken gaske, kuma in Allah ya yarda zamu dinga bijiro maku sashinsu ku ga inda suka dauki fansa a kan Annabi (saw), kuma in ka kuskura kace ba haka ba sai ya zama sai a bar asalin maudu’in, wato Annabi din sai a koma ya zuwa ga wanda a wurinsu ya fi Annabi. Hakikitan a aikace sun fi Annabi a wurinsu. Sannan Muslim ma ya fi Annabi, Bukhari ma ya fi Annabi a wurinsu. Ku karba daga gare ni in Allah ya yard azan tabbatar maku da haka, ko yanzu ya kamata ku lura AlBukhari ya fi Annabi, Muslim ya fi Annabi balle sahabbai, sun fi Annabi a wurinsu. Saboda da AlBukhari zaka dunkude mutuncin Annabi. Da Muslim zaka iya tunkude hukuncin aya a kan Annabi, WA INNAKA LA’ALA KHULUKHIN AZIM misali, WAMA YANDIKU ANIL HAWA misali.
 "To,  sun dauki fansa akan Annabi (saaw), sun kirkiri riwayoyi ba iyaka. To, yanzu su wayannan mutanen sune suke siffata wannan Annabin da cewa yana la'anta a kan fushi alhali sun rawaito wannan riwayar wadda ta inganta a wurinsu a Muslim cewa Annabi yace shedaninshi ya musulunta bai umurtanshi sai da alkhairi. Tunda yana umurtanshi da alkhairi ne kawai ya aka yi yana zagin wani?