Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : tsk
Lahadi

25 Maris 2018

05:54:15
886840

TAKARDAR SANARWAR MANEMA LABARAI

LAFIYAR SHAIKH ZAKZAKY NA CI GABA DA TABARBAREWA YAYIN DA GWAMNATI KE NUNA HALIN KO-IN-KULA

A yan kwanakin da suka gabata, mun samu labarin cewa halin lafiyar Jagoranmu, Shaikh Ibraheem Zakzaky na ci gaba da tabarbarewa a sakamakon kin ba shi damar samun kyakkyawar kulawar kwararrun likitoci ta gaggawa da yake bukata.

Shaikh Zakzaky, wanda aka harba a wurare da dama fiye da shekaru biyu da suka gabata, wanda ya yi sanadiyyar rasa idonsa na hagu, yana kuma gab da rasa dayan idon nasa na dama matukar bai samu kyakkyawar kulawar da ta dace ba. Ya kuma yi fama da rashin lafiya ta shanyewar jiki a cikin watan Janairu na wannan shekarar, a sakamakon cutarwa da muzgunawar da yake fuskanta, baya ga rashin lafiyar raunukan da aka yi masa kuma aka hana shi samun kulawar Likitoci a inda ake tsare da shi. Kuma tun sannan bai warke ba. Wannan mummunar dabia ta halin koin-kula da gwamnati ta ke nuna wa ba abin yarda da amincewa ba ne ko kuma kau da kai tare da yin shiru.

Wannan mummunan yanayi mara dadin ji da gani har yanzu bai sanya gwamnatin tarayyar Najeriya ba akalla ta bi ko da umurnin da Kotu ta bayar ba fiye da kimanin shekara guda da ta gabata, wanda ta yanke hukuncin cewa bai aikata laifin komai ba.

Mummunan aikin taaddancin Jamian tsaron gwamnati ne ya jefa shi a cikin wannan mawuyacin hali a matakin farko. Haka nan kuma rashin son gaskiya da adalci na mahukunta wannan gwamnati mai ci ta Najeriya ne ya sanya suke ci gaba da  tsare shi a cikin wannan mawuyacin hali na matsananciyar rashin lafiya da yake ciki. Haka batun ma yake ga mai dakinsa, Malama Zeenatuddeen wadda take fama da irin nata matsanancin ciwon a inda aka tsare da su.

Don haka muna shelantawa da babbar murya cewa, gwamnatin Tarayya ke da alhakin duk wani abu da ya faru da Shaikh Zakzaky da mai dakinsa a inda ake tsare da su. Ya zama dole a shaida wa gwamnati tsagwaron gaskiya.

A lokacin da muke  kira ga gwamnati da ta kiyaye alhakin da ya rataya a wuyanta na yin aiki bisa doka, muna kuma yin amfani da wannan dama wajen kara yin kira ga yan rajin kare hakkin dan Adam, Kungiyoyin kare hakkin biladama, Kungiyoyin  Kasa da Kasa da kuma daukacin alumma da su kara yin amfani da damar da suke da ita wajen ganin cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa sun samu ’yancinsu.

SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA HARKAR MUSULUNCI A NAJERIYA
Skype: Ibrahim.musa42
24/03/2018