Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : tsk
Litinin

19 Maris 2018

16:12:20
886254

YADDA LABARIN HARBIN MAHAIFINA YA RISKE NI

Muh'd Qassim (Babban dan Shaheed Qassim Umar R/Tawaye

Wannan Hira ce da aka yi da dan Shaheed Qassim, Wanda ya bayyana Muhimman abubuwa da suka faru har zuwa ga Shahadar Mahaifinsa*

TAMBAYA: Malam Muh'd zamu fara da yi maka Taaziyya na Shahadar Mahaifinku, Allah qara muku Juriya akan wannan Jarrabawa.

MUH'D QASSIM: Ilahee, Nagode.

TAMBAYA: Zamu so ko da a taqaice ne, ka bayyana mana yadda labarin Harbin da aka yiwa su Shaheed ya riske Ku, (don kamar naji Baku tare dashi a wannan lokaci).

MUH'D QASSIM: Toh, zan so na fara tun daga ranar da Labari ya fito akan halin da jikinsu Malam (H), cewa yayi tsanani, don na tuna a ranar shi ma Baba bai da lafiya, don nazo gida na iske shi kwance an masa Allura, da ya tashi nake gaya masa halin da ake ciki, sai yace lallai bai Sani ba, baa kira shi an gaya masa ba. Na gaya mishi an gaya min cewa; an tsara Muzahara zaa yi tun daga Litinin tsawon sati, saboda halin da su Malam (H) suke ciki. Na dan miko masa ruwa yasha, sai muka tashi aka tafi Markaz, aka hada Yara don ayi addu'a, sannan aka kira 'yan uwa da nufin a fita Muzahara, toh sai ya zamo 'yan uwan basu hadu kamar yadda zai yiwu a fita Muzahara ba (saboda yanayin garin namu) aka dawo gida, ya dan kwanta, zuwa Magrib ya tashi daga nan aka shirya aka tafi wani gari program (wannan shine Program nashi na Kashe), kafin labarin halin da su Malam (H) yazo, da yace ba zai je ba, saboda yanayin jikinsa, amma dai haka ya mike aka je wannan program din.

Da safe, aka yi Muzahara sai yace mana zaa yi ta yamma, daga nan ya tashi ya nufi Zaria, wurin zama na Da'iratul amm, ya tafi da niyyar zai dawo sannan ya shirya ya wuce Abuja, amma daga can sai ya kira yace a bawa wani dan uwa kayan shi ya taho masa dashi Abuja, shi ba zai dawo ba sai an saki Malam (H).
 
Ranar Talata da rana sai ya kirani, yace min an harbe shi, kuma yana tsammanin zai yi Shahada ne, daga wannan lokacin sai ya zama muna tambayar shi yanayin jikinsa, da wuraren da aka kai shi, har ya zamto ba ya iya daukar waya (Harsashin yaci Qarfin jikin shi). Daga wannan lokacin ne sai ya zamo na kama hanya da nufin Tahowa Abuja, sai kuma naga kiran shi, yace min akwai maganin shi yana tsammanin ciwon shi zai tashi na taho masa dashi, sai kuma ya kirani akan yanzu zaa taho dashi Kano, akan akwai wadanda suka shirya Visa zaa fita dashi don kula da lafiyarsa a waje (don sun nuna kada ma a taba shi (Treatment) sai an fita waje).

TAMBAYA: Ka wuce Abujan a wannan lokacin?

MUH'D QASSIM: A'a na kama hanya na taho Kano, da nufin tarbar sa anan, sun baro Abuja sun kusa Kaduna saboda zubar jinin da yayi, sai ya zamo jikinsa yayi tsanani sosai, (har ya zamo ba ya iya ma bude idonsa) sai aka yanke shawarar a tsaya nan Kaduna a saka mishi jini, washegari a taho Kano, a fita dashi, (Saboda ance an shirya komai shi kadai ake jira).

Ina nan Kano dai har Yammacin Laraba, sai can wani da suke tare ya kirani yake gaya min akwai wasu da suka zo su Dr. Tsafe, sun yanke shawara akan akwai wani likita wanda zai iya yiwa Baba aiki (Aiki na farko) kafin a fita dashi, don haka sai na tashi na nufi Kaduna, ko da naje na iske Qanina Ahmad yake gaya min an shiga da Baba dakin da zaa mishi aiki, Na jira bayan wani lokaci aka fito dashi, naje wurin shi naga halin da yake ciki. Muka kwana da nufin washegari zaa wuce Kano don a fita dashi.

TAMBAYA: Ke nan ranar Alhamis kuka baro Kaduna kenan?

MUH'D QASSIM: A'a washegari likita yazo, ya duba jikinsa (mun dauka shi kenan zaa tafi Kano) sai dai hakan bai samu ba, nan dai muna Asibitin har lahadi. Akwai abubuwa da yawa da na lura dasu a wannan Asibitin, na farko Asibitin na Sojoji ne, kamar yadda na tambayi wani da suke tare da Baba, ya Shaida min Wanda suka kawo su Asibitin sun gayawa mai Asibitin wai Baba, anyi Qoqarin Kidnapping (garkuwa) din shi ne, sai aka harbe shi, amma muna zaune wani Soja yazo ya canja TV ya kamo Alwilaya, sannan washegari da aka yi aiki, 'Marshal' (Mai Asibitin) da likita suka zo, likitan sai yace sai Baba ya miqe ya taka da Qafar da aka yiwa aikin, yayi Qoqari ya tashi ya dogara, amma Qafar ta kasa zuwa Qasa, shi kuma ya kafe akan sai ya taka Qafar, da ya matsa akan sai ya taka, sai Baba yace lallai kada mu bari ya qaraso kusa dashi don ba zai iya takawa ba.
'Marshal' din shine ya dunga magana akan Baba ya Sani fa shi Soja ne, amma yake musu magana haka?!.

Ranar Lahadi da yamma muka kama hanyar Kano, cikin Ambulance da Rakiyar Sojoji, muka isa da dare.

TAMBAYA: Lokacin da Shaheed yake Jinya, ya samu ganawa da 'yan Jarida, Wanda a wannan lokaci ya bayyana halin da ya kasance a bayan fitowar sa Gyallesu, ko me zaka ce dangane da wannan?

MUH'D QASSIM: Lallai haka ne, domin mu da muke gida a tare dashi, mun San irin damuwar da ya shiga a bayan waqiar Zaria, yana yawaita kuka sosai, dalilin kukan  kuwa shine ya fito a Gyallesu babu ko Kwarzane a jikinsa, gashi duk abunda ya samu su Malam (H) shi yana raye, har wani lokaci Kakar mu (Mahaifiyar shi) take masa magana akan wannan kukan (Ya kamata ya rage, duba da rashin Lafiyar da yake fama dashi a lokacin) Sai yayi nuni da ba zaa fahimci halin da yake shiga ba, idan ya tuna halin da Jagora (H) ya shiga, da kuma irin yanayin da yake ciki har yanzu. Lallai yana yawaita kuka sosai, da kuma yawan Roqon Shahada, yana kuma Muhimmantar da dukkan wani Abu da zaa yi shi don ganin anyi wani Qoqari ganin su Malam (H) sun kubuta daga hannun Azzalumai.

TAMBAYA: Kamar yadda ka ambata cewa, an tsara ana zuwa Kano zaa wuce dashi waje don samun cikakkiyar kulawa, sai kuma dai hakan bai samu ba, har ya zamo yayi Shahada anan (Kano), ko akwai wani Qarin bayani da zaka yi kan Musabbabin haka?

——Zamu cigaba Insha Allah