Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Taskar Alkhairi Naija
Asabar

10 Faburairu 2018

12:57:12
881404

DAWWANA HADISI A WAJEN MALAMAN SHI’AH

_______Sheikh Hamzah Muhammad Lawal Yusuf Sulaiman Ya rubuta Zama na 6(2) ….Cigaba

Mawallafin Littafin(Al-Wasa’il)  ya fara ne da hadisan muqaddimomin ibadu, wato abinda ake yi kafin a fara ibadoji. Sannan sai ya jera hadisan hukunce hukunce, wato ina so in ce sai ya jera babobin littafan akan jerin hukunce hukuncen fiqhu, wato daga Ad-Dahara zuwa Ad-Diyarat. Sai ya zama littafin Kaman littafin fiqhu yake. Sannan ana cewa kowane babi ko hadisan farko a babin zai zama wannan shine ra’ayin shi a babin, saboda haka Kaman littafin fiqhu ne.
Kai a taqaice, a cikin duniyar shi’a gabaki daya wannan shine littafi da ya fi kowane tattaro hadisan halal da haram, wato hadisan Ahkam. Duk Faqih baya wadatuwa daga Al-Wasa’il. Kuma shine littafin da yafi kowane littafin da ya fi tattaro hadisan Ahkam. Kuma shine littafin da ya fi kowane littafi kyautata jera wa’yannan hadisan na Ahkam. Saboda haka idan kana so ka samu littafin hadisan Ahkam daga Ad-Dahara ko daga muqaddimah din Ad-Dahara har zuwa Ad-Diyat me kake bugata? Kana bugatan Al-Wasaa’il.
Wa’yannan hadisan ne malamanmu suke ijtihad da istimbad a cikinsu. Su inganta, su bada ra’ayoyinsu. Har (Al-Wasaa’il) ya fi Al-Wafiy da Al-Bihar a tattaro hadisan Ahkam da kuma jera su mafi kyawun jeri. Ta ina ya fi Al-Wafiy? Ta ina ya fi Al-Bihar? Saboda taqaituwar Al-Wafiy akan tattara abinda yake a cikin Al-Kutubul Arba’a kawai kuma su akan sabanin sabawar tartibin da aka saba dasu a cikin su Al-Kutubul Arba’a din, wato ya caccakuda su, wannan dangane da Al-Wafiy kenan. Me yasa Al-Wasaa’il ya fi shi? Ya fi shi akan kyawun tartibi.
Kuma ya fi Biharul Anwar ne saboda taqaituwar shi Al-Bihar din a kan hadisan da basa cikin Al-Kutubul Arba’a. Hadisan Al-Bihar wane hadisai ne? Hadisan da basa cikin Al-Kutubl Arba’a. Amma shi Al-Wasaa’il ya hada da hadisan da suke cikin Al-Kutubul Arba’a da kuma dukka ko kusan dukkan hadisan Ahkam sannan kuma ya hada da “juda” din tartibi. Shi yasa ya fi Al-Wafiy saboda muwasaqan mu akan tartibin shi, ya fi Al-Bihar saboda taqaituwan shi da hadisan da basa cikin Al-Kutubul Arba’a.
Mu’akazan mu ta biyu akan Al-Bihar- da muka ce “mu’akaza” muna nufin bambamcin shi da Al-Wasaa’il- itace tare da cewa bugu da kari mafi yawancin hadisan shi (Al-Bihar) ba hadisan Ahkam bane- wato akwai na Ahkam amma mafi yawancin su ba na Ahkam bane. Na farko bai dogara akan Al-Kutubul Arba’a ba. Na biyu mafi yawancin hadisanshi ba akan maudu’in Ahkam bane, shi yasa muka ce Al-Wasaa’il ya fi a nan wurin.
Saboda haka dangantakan wannan “jaami’e” din- wanne Jaami’e? Al-Wasaa’il- dangane da sauran “jawaame’e” wato dukkan sauran littafan da suke a wannan kasafin wanda suka zo daga baya(wato Al-Jawaami’ul Muta’akhkhirah” shine Kaman dangantakan Al-Kafiy ya zuwa ga dukkan sauran Al-Kutubul Arba’atul Mutaqaddima. Kenan, tsaran Al-Kafiy a cikin Al-Kutubul Muta’akhkhirah shine- tsara majazan muke nufi, ba haqiqatan ba, ba tsaran shi bane saboda shi muta’akhkhir yake. Wato in kana so kace wane irin Al-Kafiy a wannan jerin? Shine Al-Wasaa’il. Al-Kafiy ya yi ma MAN LA YAHDURUHUL FAQEH da AL-ISTIBSAR da AT-TAHZIB fintinkau a marhala ta farko. Da muka ce marhala ta farko muna nufin marhala ta farko daga cikin Al-Jawaami’ul Kabirah. Al-Jawami’ul Kabira muka ce sun kasu kasha biyu; kasha na farko sune Al-Mutaqaddimah daga cikinsu, kasha na biyu kuma sune Al-Muta’akhkhirah daga cikinsu.
Al-Kafiy a cikin su hudu na farko shine sarki shine shugaba. A cikin wa’yanda suka zo a baya Al-Wasaa’il shine shugaba. A jeri na farko daga cikin Al-Jawami’ul Kabirah wanda suke Al-Mutaqaddimah babbansu shine Al-Kafiy, sannan sauran. Su kuma hudun gabaki dayansu din su kuma sun wuce a mataki wa’yannan da muke Magana akansu a yanzu, saboda haka kowane ka san yanda zaka ajiye shi. Al-Bihar da Al-Kafiy wanne ya fi wani a wajen mu?
Al-Wasa’il ya sake yin kama da Al-Kafiy kuma a mudda din da aka dauka a wurin hada shi zuwa shekara 20. Shi a cikinshi sai da aka yi shekara 20 kafin mawallafinshi ya kammala hada shi. Zaka iya duba Az-Zari’ah Ila Tasaanifish Shi’ah. Hadisi 35,850 Al-Wasa’il ya kunsa.
3. BIHARUL ANWARIL JAAMI’ATI LI DURARI AKHBARIL A’IMMATIL AD’HAR
Wannan ne muke ce mashi Biharul Anwar a taqaice. Na Ash-Sheikh Muhammad Baqir- shi yasa muke ce mashi Al-Baqirul Majlisi- dan Muhammad Taqiy Al-Majalisiy. Ya rasu a shekara ta 1,110h . Yaushe  Al-Hurrul Amuliy ya rasu? Muka ce 1,104h. Wannan shi kuma 1,110h. Al-Hurrul Amuliy ya rasu shekara 6 kafin  Al-Majlisiy.
Ash-Sheikud Dahraniy yace dangane da Al-Bihar cewa shine jaami’in littafi- da muka ce jaami’e muna nufin wanda ya tattaro- wanda ba a rubuta ba gabaninshi da kuma bayan shi wani jaami’I irinshi. Yanzu yanzu muka ce Al-Wasaa’il ya fi shi, me kake nufi da wannan? Zai fada maka me yake nufi. Ba rubuta wani jaami’I irinshi ba gabaninshi da kuma a bayanshi har zuwa yau dinka din nan. Me yasa?
Domin bayan tattaro hadisai ya kuma hada (wato Al-Bihar) da tahqiqoqi da bahsosi da ijtihadoji daqiqa yana fadin ra’ayinshi, yana bayani, darussa. Ba ardin hadisai kawai yayi ba. Bayan ardin hadisai sannan yayi ta’aliqoqi akan hadisan, wato tahqiqoqi daqiqa sosai (precise) da bayanoni da kuma sharhohi a kan hadisan. Ba kawai “mutun” ne na hadisai ba, akwai tahqiq ko tahqiqaat da bayanaat da shuruh na hadisai. Sharhohi masu tsawo. Yawanci ba a samun irin wa’yannan sa’ayin a waninshi. Wani zaka ga hadisan ne kawai.
Fihris din littafan da suke cikin Al-Bihar kaman yanda shi mawallafin da kan shi Al-Allamah Al-Majlisiy ambata a muqaddimah dinshi sune wa’yannan; Kitabul Aqliy wal Ilmi wal Jahl, Kitabut Tauhid, Kitabul Adli wal Ma’ad, Kitabul Ihtijajat wan Nazarat wa jawaami’ul Ulum, Kitabul Kisasil Anbiyah, Kitabu Tarikhi Nabiyyina wa Ahwalihi(sawa), Kitabul Imamah wa Fihi  Jawami’i Ahwali A’immatina (as), Kitabul Fitan, Kitabu Tarikhi Amiril Mu’uminin (as) wa Fada’ilihi wa Ahwalihi, Kitabu Tarikhi Fadimata wal Hasan wal Husain (as), Kitabu Tarikhi Ali Ibn Husain wa Muhammad ibn Ali Al-Baqir wa Ja’afar Ibn Muhammad As-Sadiq wa Musa Ibn Ja’afar Al-Kazim (as), Kitabu Tarikhi Aliyibni Musar Ridha wa Muhammad Ibn Ali Al-Jawad wa Ali Ibn Muhammad Al-Hadiy wa Hasan Ibn Ali Al-Askari (as), Kitabul Gaiba wa Ahwalil Hujjatil Qa’im(as), Kitabus Sama’I wal Aalam, Kitabul Imani wal Kufri wa Makarimil Akhlaq, Kitabul Adabi was Sunan, Kitabur Raudah, Kitabud Daharati was Salati, Kitabul Qur’ani wad Du’ah, Kitabuz Zakati was Saum, Kitabul Hajj, Kitabul Mazaar, Kitabul Uqudi wal Iqa’at, Kitabul Ahkam, Kitabul Ijazaat, littafai 25 kenan.
An rubuta (Al-Bihar) rubutu irin na “hajariy”, juzu’I 25 akan asasin yanda mawallafin yayi juz’o’in littafan da suke cikinshi. Sannan daga baya aka yi mashi wannan wannan bugun Kaman yanda ka gani yau, wato bugun zamani a juzu’I 110. Daga 25 sai ya koma 110 saboda irin wannan rubutun na zamani. Wannan shine na uku a wannan dabaqa din, sannan sai na hudun wanda zamu karanta shi zamu yi bayanin shi a zama na gaba.