Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Pars Today
Jummaʼa

10 Nuwamba 2017

12:35:33
865946

Miliyoyin Masoya Ahlulbaiti Na Gudanar Da Tarukan Juyayin Arba'in A Karbala

Rahotanni daga kasar Iraki na nuni da cewa miliyoyin mabiya da masoya Ahlulbaiti (a.s) daga duk fadin duniya suna ci gaba da taruwa a birnin Karbala na kasar Irakin don gudanar da juyayin Arba'in na Imam Husain (a.s) don tunawa da cikar kwanaki 40 da kisan gillan da aka yi wa Imam Husainin da iyalai da magoya bayansa a shekara ta 61 bayan hijirar Ma'aiki (s).

Rahotannin sun ce tun jiya ne dai miliyoyin mutanen suke ta isowa birnin na Karbala mafi yawansu suna tattaki daga birnin Najaf da ke kimanin kilomita 76 daga birnin Karbala din don halarta taron na Arba'in da ake ci gaba da gudanar da shi a yau din nan Juma'a.

Rahotanni daga Irakin sun ce gwamnatin kasar ta dau tsauraran matakan tsaro a garin Karbala din da kewayensa da kuma dukkanin hanyoyin shigowa garin don kiyaye lafiyar masu ziyarar daga duk wata barazana da za ta iya samun lafiyarsu.

Taron juyayin ranar Arba'in din dai ana  gudanar da shi ne a ranar 20 ga watan Safar na kowace shekara, wato kwanaki 40 bayan kisan gillan da aka yi wa Zuriyar Annabi a Karbala din a ranar 10 ga watan Muharram na shekara 61.