Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Pars Today
Alhamis

9 Nuwamba 2017

13:13:52
865720

Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Juyayin Arba'in Na Imam Husain (a.s) A Iran

Miliyoyin al'ummar kasar Iran, a duk fadin kasar, suna ci gaba da gudanar da bukukuwan juyayin ranar Arba'in na Imam Husain (a.s) don tunawa da abin da ya sami zuriyar Ma'aiki (s) karkashin jagorancin Imam Husaini (a.s) a Karbala na kasar Iraki.

Rahotanni daga bangarori daban-daban na kasar Iran din sun bayyana cewar tun da safiyar yau Alhamis ne miliyoyin masoya Ahlulbaitin Annabi (s) cikin bakaken kaya da sauran nau'oi na alamun nuna juyayi don nuna alnihi ga abin da ya sami Imam Husain (a.s) da iyalai da mabiyansa a shekara ta 61 bayan hijirar Ma'aiki.

A nan Tehran ma dai an gudanar da irin wadannan bukukuwan juyayin a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) da ke gidan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei inda dubun dubatan daliban jami'a suka taru don nuna alhininsu.

Bikin ranar Arba'in din dai ana  gudanar da shi ne a ranar 20 ga watan Safar na kowace shekara, wato kwanaki 40 bayan kisan gillan da aka yi wa Zuriyar Annabi a Karbala din a ranar 10 ga watan Muharram na shekara 61.