Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Taskar Alkhairi Naija
Asabar

22 Yuli 2017

20:00:13
843680

Hardace Alkur’ani ga yara abin farin ciki ne da Murna _____Inji Sheikh Yakubu Yahaya Katsina

Yau Asabar 22 ga watan Yuli 2017 ne,Fudiyya Tahfiz Kano ta yi bukin yaye dalibai mahaddata Alkur’ani a filin Dantata dake Dandishe Kano. Sheikh Yakubu Yahaya Katsina a lokacin da yake gabatar da jawabi a matsayin babban bako a wajen bikin ya bayyana cewa hardace Alkur’ani ga yara abin farin ciki ne da murna. Malamin yayi nasiha da jan hankali ga daliban da suka haddace Alkur’anin da kuma Malaman su daliban.Sannan ya nuna muhimmancin samar da makaranta ta tafsirin Alkur’ani mai girma domin ka da a bar yaran su tafi haka nan don sun yi sauka. Sannan ya tabbatar da cewa a cikin rahoton da turawan mulkin mallaka suka kaiwa iyayen gidansu,akwai cewa yankin gabas (Borno)wuri ne da ake samun ilmin Alkur’ani shi yasa ake neman tarwatsa yankin.Yanzu ta bayyana karara ana fada da Alkur’ani ne,sannan ita kuma hukuma tana so ta kashe tasirin karatun Alkur’ani a cikin al’umma. Malamin yayi kira ga mawadata a cikin harka da su taimaka ma makarantun Fudiyya,yana cewa: “Su Malam na fada mana cewa mutum ya kure iyakar abinda yake iya yi domin neman sakamako a lahira.” Ya kara da cewa: “Su Sayyida sun bada lakani cewa idan kana bayarwa (wato infaqi) to Allah zai nunnuka maka abinda kake bayarwa din.” Sannan Malamin ya kirayi ‘yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky da suyi ilimin boko amma lokaci guda kada a bar ilimin Alkur’ani domin dukkansu ilimi ne kuma ana yin ilimi domin Allah ne.Yana cewa: “Shi karatu ana yinsa domin Allah ne,idan aka cire Allah a cikin karatu,to,komai sai ya dame ma mutum.” A karshe yayi kira da ‘yan uwa su hada kansu yana cewa: “Mu kara riko da junan mu,mu girmama ra’ayin juna.Duk ayyukanmu na gayya ne,duk inda muke mu yiwa juna uzuri.A iya sani na babu wani dan uwa wanda yake wani aiki don rugujewar harka,kowa na yin iya kokarinsa domin cigaban harka.” Bukin ya samu halartan wakilan ‘yan uwa na garuruwa da dama da sauran ‘yan uwa daga sassa daban daban na kasan nan.

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano

Kano