Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Taskar Alkhairi Naija
Laraba

19 Yuli 2017

17:40:29
843132

Shari’ar ‘Yan uwan da aka kama a Zariya:Har yanzu ba tabbatar da laifin ‘yan uwan da aka kama a Zariya ba ____Inji Festus Okoye

A jiya talata,18 ga watan Yuli 2017 ne aka cigaba da shari’ar ‘yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky wa’yanda aka kama a lokacin da sojoji suka kai hari gidan Sheikh Zakzaky da Husainiyyah da Darur Rahma a watan Disamban 2015. Alkali David Shiri Nyom a babban kotun jihar Kaduna ne ya cigaba da sauraron shedu guda biyu daga rundunar soja wadanda suka dinga tubka da warwara a zancensu a lokacin da lauyoyin Harkar Musulunci suke masu tambayoyi. Daya daga cikin masu gabatar da shedan mai suna Birgediyya Janar A K Ibrahim yayi tubka da warwara a lokacin da yake bada labarin shigan shi Zariya a ranar 12 ga watan Disambar 2015.Ya fada ma kotu cewa ya shiga Zariya a wannan ranar da misalin karfe 5:30 na yamma,sai daga baya ya karyata shigan shi Zariya a wannan lokacin da ya fadi(wato 5:30) a lokacin da lauyan ‘yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky yake mashi tambayoyi,yana cewa a’a,shi da karfe 6:00 ne ya shiga Zariya sabanin 5:30. Dayan shedan kuma sunansa Laftanal Kanal Ali.Ya fadi a lokacin da yake bada sheda cewa makaman da suka samu a wajen daliban Sheikh Zakzaky sun mikawa ‘yan sanda a ranar 13 ga watan Disambar 2015 wanda ya saba da bayanin da Lauya Festus ya bayar akan cewa an mikawa ‘yan sanda makaman ne a ranar 9 ga watan Febrerun 2016. Kanal Ali yace ba zai yi mamaki ba idan ya zama cewa an mikawa ‘yan sanda wadannan makaman ne a wannan ranar da Festus Okoye ya fadi sabanin yanda ya fadi. Kaduna DPP,Dari ya fadawa manema labarai a lokacin da aka fito daga kotun cewa yana jin dadin yanda shari’ar take gudana. Festus Okoye a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai ya fadi cewa: “Mu abinda ya dame mu shine har yanzu wadanda ake zargi suna nan a kubutattu tunda ba a iya tabbatar da laifinsu ba.Kuma masu zargi sun gajiya wajen tabbatar da laifin wadanda ake zargi.Amma dai Alkali ne yake da magana ta karshe.” A karshe dai Alkali David ya dage shari’ar zuwa 8 da 9 ga watan Agusta 2017.A wannan ranar a sa ran za a gabatar da karin wasu shedun.

Kotu

Kotu

Kotu