Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Taskar Alkhairi Naija
Laraba

5 Yuli 2017

18:06:43
840642

JAMI’AN TSARO A NIGERIYA SUN ANTAYAWA DALIBAI MASU MUZAHARAN NEMAN A SAKI SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY A ABUJA NIGEIYA

Tun bayan waqi’ar da ta faru a garin Zariya a watan Disamban 2015,wadda tayi sanadiyyar rasuwar daruruwan mabiya babban malamin Shi’a a Nigeriya mai suna Sheikh Ibrahim Zakzaky ne,kungiyar Dalibai na Harkar Musulunci a Nigeriya suke fitowa suna muzaharori domin nuna rashin amincewarsu da aika aikan da akayi masu da kuma cigaba da tsare Jagoransu ba tare da wani haqqi ba musamman ma da babban kotun tarayya tayi umurni da saki malamin amma gwamnati tayi biris ta wannan umurni na Kotu. Yau ma kaman sauran lokutan baya,wa’yannan dalibai karkashin wannan kungiyar ta dalibai sun fito domin neman a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky a garin na Abuja Nigeriya. Wa’yannan dalibai sun fito cikin tsari da nizami kaman yanda suka saba fitowa a lokutan baya.Daliban sun dauko muzaharan ne daga bakin kasuwar UTC dake Area 10 dauke da banoni da kwalaye wa’yanda aka rubuta “free Zakzaky” a jikinsu,suna rera wakoki na kira ga gwamnatin Nigeriya karkashin shugabancin muqaddishin Shugaban Kasa da ya bi umurnin kotu ya saki Sheikh Zakzaky wanda yanzu yake neman shekara biyu a tsare ba tare da wani laifi ba. Muzaharan ta biyo ta wajen “Art and Culture” har zuwa hanyar da zai kai ga Area 1.Karasowar masu muzaharan ke da wuya kasuwan Area 1 ne,kawai sai jami’an tsaro suka zo suka fara harbo barkonon tsohuwa akan masu muzaharan. Masu muzaharan sun rufe muzaharan a wannan kasuwa ta Area 1,kowa ya watse.Har zuwa hada wannan labari bamu da labarin kama wani daga cikin masu muzaharan.

Abuja

Abuja

Abuja