Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Tomasa Kuwaisi Karti mataimakin babban sakataren kungiyar tarayyar Afrika yana fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa wannan batun yana daga cikin batutuwan da shuwagabannin kasashen AU zasu tattauna a taronsu na 29 da zasu fara a yau litinin a birnin Addis -Ababa cibiyar kungiyar ta AU.
Tomas ya kara da cewa tsarin kwamitin tsaro a halin yanzu na yanayin duniya bayan yakin duniya na biyu ne, ya kuma kara da cewa a halin yanzu duniya ta canza, don haka ya kamata a gabatar da sauye -sauye a cikin majalisar daga cikin akwai butar a bawa kasashen Afrika kujerun din-din-din guda biyu sannan wasu karin kujeru 5 na wucin gadi a kwamitin tsaro.
A shekara ta 2005 ma kasashen Afrila sun bukaci a gabatar da sauye sauyye a tsarin tafiyar da majalisar dinkin duniya don ya tafi dai dai da sauye sauyen da aka sami a duniya tun bayan yakin duniya na biyu.