Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Taskar Alkhairi Naija
Asabar

1 Yuli 2017

14:07:30
839803

AN CIGABA DA SAURARON KARAR DA SHEIKH ZAKZAKY YA SHIGAR A BABBAN KOTUN KADUNA

Kaman yanda aka sani jiya Juma’a 30 ga watan 2017 ne Alkalin babban kotun Kaduna ta sanya domin cigaba da sauraren karar da Sheikh Ibrahim Zakzaky ya shigar a kotun,yana karar rundunar sojan Nigeriya da Antoni janar na tarayya da kuma gwamnatin jihar Kaduna.

Sheikh Zakzaky ya shigar da Shugaban rundunar Sojan Nigeriya,Laftanan Janar Tukur Yusuf Burutai,Antoni Janar na tarayya,AGG,da kuma gwamnatin jihar Kaduna babbar kotun Tarayya domin kashe masa ‘ya’ya da rushe masa gida.
A lokacin da lauyan gwamnatin tarayya ta bugaci kotu da ta yi watsi da wannan karar saboda kaman ana maimaita irinta da aka yi a Abuja ne.Amma Alkalin babban kotun,Alkali Saleh Musa Shu’aibu ya nuna mata cewa akwai bambamci tsakanin wannan shari’ar da aka yi a Abuja da wadda ke gabansa a yanzu,yana cewa: “Na bibiyyi hukuncin da kwararren abokina a yanke a Abuja,wato Alkali Kolawole wanda yayi hukuncinsa akan tsarewa ba akan ka’ida ba da kuma tauye hakkokin Sheikh da mai dakinsa Malama Zeenat.
“Ni abinda ya dame ni a nan shine zan yi hukunci ne akan rushe masu gidaje da kayayyaki da kuma kashe ‘ya’yan mai karan wanda aka kawo min.”
Lauyan soja ya nemi a bashi dama yayi magana akan abinda lauyan gwamnatin tarayya ta fada,amma Alkali ya yace ba zai ba shi dama ba saboda wannan ya saba ka’idar kotu .
Shi kuwa Lauyan gwamnatin Kaduna,Barista Bayero Dari ya bayyana cewa ya aminta da abinda lauyan gwamnatin tarayya da na soja suka gabatar.
Mr Festus Okoye ya nuna rashin jin dadinsa game da maganar cewa Sheikh Zakzaky bai sa su kare shi ba a kotu.Amma Alkali ya bayyana cewa an yi ta kawo maganar a kotun tarayya ta Abuja kuma lauyoyin gwamnati sun gudu da suka ga Alkali Kolawole zai nemi da a kawo Sheikh Zakzaky kotu.Alkalin ya tabbatar da cewa ya aminta dasu Festus Okoye a matsayin masu kare Sheikh Zakzaky .
Festus Okoya ya kara da cewa wannan shari’ar ba iri daya bace da ta Abuja,sabanin abinda lauyoyin Soja da gwamnatin tarayya da jihar Kaduna suka fadi.Alkali ya bayyana cewa ya san haka,sannan ya kara da cewa kun je Abuja ne saboda kalubalantar tsare Sheikh ba a kan ka’ida ba,sannan kunzo wannan kotun na nawa domin kashe ‘ya’yansa da kuma rushe masu mahalli wanda a nan jihar aka yi.Sai Lauya Festus ya tabbatar da cewa ee.
Bayan tattaunawa da muhawara mai tsawo da tsanani,Alkali Shu’aibu ya dage karan zuwa ranar 6 ga watan Juli 2017  domin yanke hukunci.
In ba a manta ba Alkalin babban kotun Tarayya dake Abuja,Alkali Kolawole yayi hukunci a 2 ga watan Disambar 2016 da a saki Sheikh Zakzaky da mai dakinsa,sannan a biya su N50m,sannan a samar masa da gida a duk in da yake so kuma a bashi tsaro.
Amma abin ban takaici har zuwa yanzu gwamnatin tarayya ta bi wannan umurni ba.

Kotu

Kotu

Kotu

Kotu