Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Taskar Alkhairi Naija
Asabar

17 Yuni 2017

15:21:10
837055

SHAHADAR AMIRUL MUMININ ALI IBN ABI TALIB

Sheikh Yakubu Yahaya Katsina yayi jawabi dangane da Shahadar Imam Ali (as) a markazin ‘yan uwa almajiran Shaikh Ibrahim Zakzaky A Ranar Juma’a,21 ga watan Ramadaan.Malamin ya karanto hadisai masu yawa dangane da faloli da darajojin Imam Ali.Daga cikin riwayoyin da ya karanta na falalan Imam Ali akwai cewa: “ babu wanda zai tsallake siradi sai wanda Ali ya rubuta ya sa masa hannu a passport kafin ka ya tsallake siradi”

A lokacin da malamin yake sharhin wannan hadisin sai yake cewa:
“Wacce irin asara aka yi duniyan musulmi?da yawa,saidai ba a makara ba,wadanda suka gabata kuma muna fata Allah ya amshi uzurinsu.Iyayen mu da kakannin mu suna da uzuri domin yadda suka samu kansu su daidai wannan lokacin iyakar ilimi da ya zo masu kenan,iyakar abinda suka sani kenan,kuma suka bautawa Allah tsakani da Allah.Saboda haka muna fata Allah amshi uzurinsu da namu gaba daya.
“Mu yanzu da ilimi ya zo ya iske mu da ilimin da aka daddanne shi sama da shekara 1000 don kada ya fito,sai lokacinmu aka jarrabe mu da fitowan wannan ilimi,to bamu da uzuri.Amma su da basu ji ilimin ba a lokacinsu,suna da uzuri amma mu bamu da uzuri,gaskiyar magana kenan.”
A lokacin da Shehin Malamin yake bayanin yanda Imam Ali ya koma zuwa ga Ubangijinsa,sai yace:
“Kafin (Imam Ali) ya cika sai ya tattaro mutane,yana ce masu akwai dan abinda za a sha?da aka zo masa da nono a cikin dan akushi sai ya sha kadan,yace kun ga wannan nonon da na sha karshen arziki na ruwa na rayuwar duniya,wato an gama,shi ke nan.
“Sannan sai (Imam Ali) ya kirawo kan ‘ya’yansa da sunansu,wane,wane ,wance,babba da karami.Yace ina maku bankwana,na bar Allah shine kalifa na akanku.Ina maku bankwana sai mun hadu gaban Allah.Sai Imam Hasan yace: Ya baba me yasa kake irin wannan magana?Na ga kakanka Manzon Allah cikin barci kamin wannan abin ya faru,ana gobe zai faru,na koka mashi nace Ya Rasulallahi ina cikin matsala,ina cikin damuwa,ina cikin takaici al’umman nan ta kai nig a bango,Ya Rasulallahi ka masu addu’a in huta dasu,Allah ka musanya masu wanda yafi sharri daga ni.Wato in suna ganin ni sharri ne,Allah ka musanya masu da wanda ya fi sharri daga gare ni,ni kuma ka musanya min da wadanda suka fi alkhairi daga su.Sai Manzon Allah yace ai wannan addu’a da kayi a cikin mafarki Allah ya riga ya amsa.Yau saura kwana uku ka iske su,kuma yau kwana ukun sun cika.
“Ya baban Muhammad me kake ma kuka?Ni daga gare ku nake ku daga gare ni kuke.Sannan sai ya waiwaya zuwa ga sauran ‘ya’yansa wa’yanda ba suna cikin ‘ya’yan Fadima(as) bane yayi masu wasiyya da ka da su saba ma Hasan da Husain,sune manya kuma sune tafiyar da lamurra ya rataya a wuyansu,don haka ku saurara masu.
“Sannan sai yace Allah ya kara maku hakuri.A cikin daren nan zan bar duniya,yau zan riske masoyi na Manzon Allah,kaman yau yayi min alkawari,bayan kwana uku,yau sun cika.Sai aka kawo takarda rubuta wannan shine wasiyyar Aliyu dan Abi Talib dan uwan Manzon Allah (sawa) dan amminsa,sahibinsa.
“Farkon wasiyya ta na shaida “la’ilaha illallah wa anna Muhammadar Rasulillah”,Allah ya sabe shi da alkhairansa,Allah ya tashi wa’yanda suke cikin kabura.Sannan ina maka wasiyya ya dana Hasan,kuma ya isa ya zama maka wasiyya da abinda Manzon Allah yayi min wasiyya.Ka ji ka ji amma in wannan lokacin ya zo zauna gidanka.Kayi kukan kurakuranka.Kar kasa duniya gaba ta zama itace abin neman ka.Ka tsare sallah cikin lokacinta,wato da lokaci yayi ka tashi kayi sallah.
“Kuma ka ba da zakka ga wa’yanda suka dace a mahallin da ya dace a bada ta.In al’amari ya rikice kayi shiru kar kace komai ,da kuma tsakaitawa a cikin al’amuran rayuwa,da adalci ko kana fushi ko kana halin yarda ka da ka zalunci wani,ka zama mai kyakkyawan makwabtaka,ka mutunta bako,wanda ka ganshi cikin halin kakani kayi ka tausaya mashi,da ma’abuta lalurori,ka sadar da zumunci,ka so miskinai ka kuma zauna tare da su,saboda haka suka zama masu tausayi-An ganshi wata rana Imam Hasan yana cin abinci in yayi lauma guda sai ya wurga ma kare lauma guda,sai aka ce Yabna Rasulillah ya kuke cin abinci da kare?sai yace ina jin kunya Allah ya ga mai rai yana kallo na ina ci ban bashi ba-Sai Imam cigaba da cewa;da tawadi’u ,ka taqaita buri,ka ta ambaton mutuwa,ku guji duniya,ko da yaushe mutuwa na iya iske ka,bala’I na iya fado maka,rashin lafiya na iya afko maka.
“Sai yace idan na cika Ya Aba Muhammad ka wanke ni,ka min likkafani,ka sa min turare da sauran turaren Manzon Allah yana nan a adane ka zuba min,wanda Jibrilu ya zo dashi domin daga Aljanna aka zo da shi.Sannan ka dora ni akan gado na.Ka da wanda ya shiga gaba gadon gawa da za a dauke ni.In kun ajiye ni kuka zo ku dora ni akan anna’ashi,to,ku dauki bayan domin akwai masu dauka ko da baku gansu ba,duk inda aka ajiye gaban ku ajiye bayan.Haka kuwa aka yi .In da kuka ga an tsaya cak tafiya ta tsaya,to,nan ne mahallin kabari na.
“Sannan ka mani sallah,ka mani kabbara bakwai,ka sani cewa ba wanda za a ma kabbara bakwai sai idan wani mutum wanda zai fito karshen zamani Al-Qa’imul Mahdi dan dan uwanka ne,shima kabbara bakwai za a yi mai.Idan ka min sallah a dauke gadon a maida shi gefe guda,sannan ku tona daidai inda aka ajiye kabarin zaku ga kabari shirye an gina an gyara kuma anyi kofa ta lahad wanda za a tura a rufe,zaku ga wato ainihin gadon gawa,ku kwantar dani.In ka gama rufe ni zaka neme ni baka ganni ba,an yi wani waje dani,zan tafi wajen Kakanka Manzon Allah kai tsaye”288