Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Abna.ir
Talata

23 Mayu 2017

19:37:20
831518

Cibiyar Ahlul-Baiting ta Duniya Tayi Allah Wadai da Harin Jami'an Tsaron Bahrain kan Shekh Isah Qasim

Bayan ziyarar shugaban kasar Amurka zuwa Saudiya da gabatar da zama domin yaki da ta'addanci wanda ba da gaske suke ba sai ga shi sun ba hukumomin Bahrain damar keta hakkin Shekh Isah Qasim

Kamfanin labarai na Ahlul-baiti-(a.s)-abna-ya lakato cibiyar Ahlul-baiti-(a.s)-ta Duniya tayi Allah wadai da harin hukumomin Bahrain kan gidan Shekh Isah Qasim. ga bayanin kamar haka

Hukumomin alikhalifa bayan takurawa ta tsawon shekara daya daga karshe a safiyar yau sun kai farmakin zalunci kan mutanen da basu dauke da makami kuma suka keta alfarma Shehu malami a gidansa da ke yankin aldaraz, a wannan harin wanda Amruka da hk.Isa'ila ke koyama baya yayi sanadiyar shahadar mutun daya inda da dama suka samu raunuka, bayan haka sun kama malamin sun tafi da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Cibiyar Ahlul-baiti (a.s) ta Duniya wadda ke da wakilai daga kasashen duniya na yin to fin Allah wadai kan wannan hari.

1-wannan harin da hukumomin alikhalifa suka kai ya faru ne sakamakon shi run da Duniya tayi na tsawon shekara shida ana kashe mutane,dari, ko rauni da sauran su wanda da tun farko kasashe masu ruwa da tsaki sun tanka ta wannan abunda ya faru yau na kai hari gidan wannan bawa Allah bai faru ba.

2-hukumar Bahrain tsawon shekara daya kenan ta kwace yan kasancin Shehu malami da wasu mutane 470 mafiya yawansu masana ne da malamai, kuma tun wannan lokacin suka so kama malamin amma dandalin mutane dake fadin gidan ya hana haka su ta cimma ruwa amma bayan ziyarar shugaba Amruka zuwa Saudiya da zama da shugabannin larabawa wannan damar ta samu ta kai harin.

3-saboda haka duniya ta sani ran shekh Isah na kan Amruka Saudiya wadanda suka dauki tsawon zamani suna goyan bayan hukumar Bahrain ta yadda har sojojinsu suka tura domin murkushe masu neman yan cin su .

4-matasan Bahrain duk da cewa basu da yawa amma sun nuna jaruntaka kuma sun can can ci yabo inda suka dauki tsawon wata sha daya suna kare gidan malamin su da addininsu.

5-daga karshe muna gargadi ga majalisar dinkin duniya,tarayyar turai, kungiyar musulmin duniya, masu fafutikar rain kare dan adam da su dauki matakin gaggawa na gani an saki malamin ba tare da wani sharadi ba in ba haka ba kasar zata shiga mugun mawuyacin hali.

Allah yana tare da wadanda a ka zauna. 

Cibiyar Ahlul-baiti (a.s) ta duniya.288