Tanadin Arzikin Halal
Uba shi ne yake daukar nauyin uwa da 'ya'ya,
don haka ya zama dole ne ya yi tanadin
abincin halal garesu domin gina musu jiki mai
lafiya ta hanyar halal, kuma wannan shi ne zai
sanya albarka a cikin rayuwarsu. Mu sani
cewa; abinci yana da tasiri mai yawa a cikin
jiki da ruhin mutum, kuma yana da babbar
rawa da yake takawa a kan tarbiyyar yara na
Sannan tasirin abinci kan yaro yana farawa
ne tun yana cikin mahaifiyarsa, wannan
al'amari ne da addini, da ilimin zamani ya
tabbatar da shi.
Sannan kuma shari'a ta yi umarni da yalwata
wa yara da dukkan iyali wajen ciyarwa da
tufatarwa, babu kwauro, babu barna, kuma
daidai gwargwadon hali, kada a tsananta kan
yara, kuma dukkan wadannan abubuwan suna
da tasiri mai yawa wajen tarbiyyar yara na
Samar Da Wani Yanayi Mai Sanya
Nishadi
Daya daga cikin ma muhimmancin bukatun
yara shi ne samar da hanyar reno da tarbiyya
mai kyau, yanayin da yake na farin ciki da
nishadi ga yaro da nuna kauna da soyayya shi
- ne na farko a muhimmanci. Kuma ya hau kan
iyaye su tabbatar da cewa ba su hana yara
wannan yanayin ba, abubuwan da sukan iya
samar da wannan yanayi mai tasiri a tarbiyya
suna iya hadawa da kyakkyawan hali, da nuna
kauna ga yaro, yin wasa da yara da raha, da
kuma sanya su farin ciki da annashuwa.
Iyayen da suke damuwa da tarbiyyar yaransu
ba zasu taba dora haushin fushinsu ko bakin
cikinsu ko daukar fansar haka a kan yara ba,
domin wani babban abin takaici wani lokaci
iyaye sukan samu bakin ciki sai su huce
haushinsa kan yaransu da ba su ji ba su gani
Iyaye masu kishin tarbiyya ta gari ba sa
lalata wa 'ya'yansu yanayi mai kyau na farin
ciki kuma ba sa gurbata musu shi.
Sannan kuma suna kokarin ganin sun boye
wannan bakin cikin ne a cikin zukatansu, sai
kuma su bayyanar da farin ciki da annashuwa
a fusakunsu. Ya zo a wata ruwaya cewa;
"Mumini shi ne wanda yake farin cikinsa yana
fuskarsa, bakin cikinsa yana zuciyarsa
.