Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : HAIDAR CENTER ACADEMY
Laraba

25 Janairu 2017

18:21:07
807248

RAYUWAR MA’AURATA KARO NA 6

Na Hafiz Muhammad Sa'id

 BANGARE NA UKU

A wannan bangaren muna kawo muku bayanai kan abin da ya shafi "Auren mace fiye da Daya" bisa mahangar al'adu da musulunci da hikimar zartar da shi har zuwa hudu a musulunci, da soke-soke da suka babaye shi tare da amsoshinsu, hada da bayanin sukan yawan matan fiyaiyen halitta da amsar hakan. Lamari ne da ya samu kallo iri-iri da suka doru kan al'adu ko bahasin amfaninsa da rashin amfaninsa a cikin al'ummu, sai dai mafi muhimmanci shi ne mayar da lamarin bisa maslahar al'ummu da kasashe tare da la'akari da zamani da wuri.

AUREN MACE FIYE DA DAYA

Allah madaukaki yana cewa: “Kuma idan kuka ji tsoron ba zaku yi adalci ba a game da marayu, to sai ku auri abin da ya yi muku dadi daga mata, biyu-biyu, uku-uku, da hudu-hudu, amma idan kuka ji tsoron ba zaku yi adalci ba, to (ku auri mace) daya ko abin da hannayenku suka mallaka….

Musulunci ya halatta auren mace sama da daya sakamakon yana son ya yi iyaka ga abin da ya taras na auren mata barkatai ba tare da wata iyaka ba, don haka yin auren mace sama da daya bai samo asali daga musulunci ba sai dai musulunci ya yi kokarin ganin yi wa abin iyaka da hudu ne daidai maslahar da Allah (s.w.t) mahaliccin mutum ya gani. Bayan iyaka da musulunci ya bayar sai kuma ya sanya sharadin adalci a ciki, don haka ba kowane mutum ne zai auri mace sama da daya ba sai wanda yake da hujjar zai iya adalci. Wannan adalcin idan ya kasance da ma’anar da ya zo a fikihu ne, to zai yi wahala a samu masu damar yin mace sama da daya ke nan sai daidaiku matukar gaske. Amma idan ya kasance yana nufin iyakacin tsakanin matan to wannan zai iya bude kofa ga wasu mutane da zasu iya haka ne kawai. Sannan ta wani bangaren kuma sharadi ne sai mace ta yarda a duk aure kowane iri ne, wannan sharadi hakki ne na mace da zata yi aure ko da kuwa da wanda ba shi da mata ne. Don haka da zata ce ba ta yarda ta auri mai mata ba, da ba ta yi laifi ba a mahangar musulunci, haka nan da namiji ya ki auren mace sama da daya a shari’ar musulunci bai yi laifi ba.

Wannan yana nuna cewa dokar an sanya ta ne don wanda suka ga dama kuma zasu iya, asali ma da wani ya ce ba zai yi aure ba bai yi laifi a shar’ance ba matukar zai iya kare kansa da kamewa daga fasadi sai dai ya bar sunnar annabi (s.a.w) mai karfi. Musulunci yana ganin halaccin auren mata har hudu a aure na da'imi, sai dai da sharadin adalci tsakaninsu, da wannan ne musulunci ya warware matsalar mata marasa aure da zaurawa, kuma abin da aka sani a cikin al'umma wanda ya tabbata a ilmance shi ne cewa a mafi yawan al'ummu mata sun fi maza yawa, idan da babu wannan doka to wannan yana nufin mata da yawa su zama ba su da ma'aurata.

Musulunci ya gindaya sharadin adalci tsakanin mata a zaman tare, da kwanan daki, da ciyarwa, ba kowa zai iya ciyar da ko da biyu ba sai mai yalwa, sannan kuma akwai hanya ta addini ta shari’a da mace za ta iya sanyawa na ka da a yi mata kishiya, kamar idan ba ta so kuma suka yi sharadi yayin aure kan cewa ba zai mata kishiya ba to dole ne ya kiyaye sharadin matukar wannan bai saba wa dokar nan ta “Sai dai sharadin da ya halatta haram ko ya haramta halal, ko da yake wannan mas'ala ce da aka yi sabani tsakanin malamai.

Auren mace fiye da daya wani abu ne da ya kasance mahallin binciken malamai da masana a wannan zamani ta yadda ya kasance duniya tana ganin sa a matsayin wani abu na danne hakkin mace, kuma tun da musulunci ya baiyanar da halaccinsa a fili don haka ne ya kasance abin suka ga masu binciken hakkin dan'adam musamman a kasashen yammacin duniya. Ga dukan alamu sukan da yammancin duniya yake yi wa musulunci sakamakon wannan lamarin na auren mace fiye da daya saboda tasirin al'adun da suke ciki ne na hanin auren mace fiye da daya da Coci ta yi ne. Sai suka taso ba su san da shi a cikin al'adunsu na yau ba, don haka ne ya kasance abin tattaunawa a teburin bincike kan hakkin dan'adam musamman mace.

A bisa hakika akwai tasirin mazhaba, addini, da ala'adu a cikin sukan wannan lamari da suke yi, ta yadda ko da kuwa zai kasance hanya ce ta warware matsalolin zaman tare da ta al'umma to ba zai samu karbuwa ba domin wani abu ne da ya saba wa al’adar yammacin duniya. Kuma kamar yadda Imam Ali (a.s) yake cewa: "Mutane makiya abin da suka jahilta ne. zamu ga yammancin duniya yana kin wannan lamarin saboda ya jahilce shi ko ya tsane shi.

Ko da yake a yau hatta da wasu masanan musulmi sun fara binciken cewa shin halaccin yin auren mace fiye da daya ya kebanta da lokacin Annabi (s.a.w) ne, ko kuwa yana nan har a wannan zamanin. Wannan kuwa yana da tasiri da yanayin da duniya ta samu kanta a ciki na wayewar zamani. Ta yadda wasu suna ganin idan nan gaba duniya ta kasance duk ko'ina musulunci ne to zai iya yiwuwa wannan dokar ta fadi. Sai dai idan mun duba abin da ya zo na cewa: "Halal din Muhammad halal ne har zuwa ranar kiyama, haram dinsa haramun ne har zuwa ranar kiyama. Zamu samu amsar cewa lallai wannan bai kebanta da lokacin Annabi ba kamar yadda bai kebanta da wadancan mutane da suka rayu tare da shi ba.

Wani abin da ya sanya wadannan soke-soken shi ne; Yammancin duniya sun kalli musulmi ne da suka yi mummunan amfani da wannan doka ta halaccin auren mace fiye da daya, ta yadda a wasu yankunan ko gun wasu mutanen ya kasance an dauke shi domin biyan bukatun sha'awar duniya. Hada da wani lokacin sukan fifita wata a kan wata sai a samu gaba tsakanin matan da kuma 'ya'yansu da aka fi sani da 'ya'yan kishiyoyi. Sai maimakon su soki abin da wadancan musulmin suke yi da ya saba wa musuluncin sai suka koma sukan ainihin musuluncin. Hada da cewa addinin Kiristanci da shi ne ya yadu a yammacin duniya yana gasa da musulunci duk inda yake a matsayin wani addini da zai iya samun ci gaba fiye da duk wani addini. Musamman idan mun duba cewa; musulunci ya hada duk abin da ya shafi duniya da lahira ne, kuma wadannan abubuwa biyu ne ya sanya su gaba da shi domin yana da hanyar da ta bambata da hanyar da suka nuna wa duniya a matsayin hanyar warware wa dan'adam abin da yake damun sa.