Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : HAIDAR CENTER ACADEMY
Asabar

14 Janairu 2017

13:50:33
804825

IYAYE DA ‘YA’YANSU Kashi Na 5

LITTAFIN: ALAKAR IYAYE DA ‘YA’YANSU Na Hafiz Muhammad Sa'id

Karfafa Izzar Rai

Daya daga cikin matsalolin da samari da yara suke fama da su shi ne; rashin samun dogaro da kai, da jin daukaka a cikin ransu, wannan kuwa yana sanya su jin tsoron shiga cikin al’umma da bayyanar da baiwar da Allah ya huwace musu ta ilimi da fasaha, hada da rashin karbar wani nauyi da aka dora musu, kuma da yawa daga rashin dacewa, da rashin cin nasara, da rashin samun ci gaba, sun faru ne sakamakon hakan, musamman yayin da sukan ji cewa su wulakantantu ne kas-kantattu ba zasu iya tabuka komai ba.

Don haka ne ma jin daukaka a cikin rai daya daga cikin mafi muhimmancin abubuwa ne da ake iya amfani da su wajen tarbiyyantar da yara, da kuma samar da yanayi mai dacewa don cigabansu da na al’ummarsu. Wannan wata siffa ce, kuma hakki da ya hau kan iyaye su ga sun kafa a cikin zukatan ‘ya’yansu, kuma wannan yana iya yiwuwa ta hanyoyi daban-daban.

Girmama ‘ya’ya, da ba su kima, da mu’amala da su a matsayin cikakkun mutane, suna daga cikin hanyoyin da za a iya karfafa wanna siffa mai kima da muhimmanci garesu.

 Bukatar Tausasawa Da Nuna Kauna

Daya daga cikin bala’o’in da wannan duniyar tamu ta yau take fuskanta shi ne; kasancewar duniyarmu ta ci gaban kere-kere ce, sai wannan lamarin ya kai ga daukar 'ya'ya da iyaye tamkar kayan kere-keren ci gaban zamani, wannan kuwa ya sanya mana fadawa cikin matsaloli da ba sa kirguwa, mafi girman matsalar yara da samari a yau shi ne karancin tausayawa, da nuna kauna da so da suka fuskanta daga wurin iyaye. Mu sani cewa; yara kamar yadda suke bukatar abinci da ruwan sha, da tufafin sawa, haka nan ma suna matukar bukatar nuna kauna da so daga iyaye fiye da wadancan abubuwan da muka lissafa.

Daya daga cikin mafi munin abin da ya fuskanci wannan duniyar shi ne; karancin soyayya daga bangaren iyaye da ‘ya’ya, kuma wannan ya haifar da tazara tsakaninsu, ta yadda ba a iya samun dasa kyakkyawar tarbiyya da halaye na gari da jin daukar nauyin hidima ga al’umma ga samarin yau. Wannan kuwa yana faruwa ne sakamakon dabi’ar fushi da kansa, da gidansu, da iyalansa, da yake cike a zuciyarsa sakamakon wancan tarbiyya ta karancin alakar soyayya da take tsakaninsu da iyayensu.

Rashin samun kauna yana kai wa ga yara da samari su ji wulakantuwa a cikin ransu, kuma su rasa jin girma a cikin zukatansu, kuma da wannan ne a hankali sai mutuncin su ya zube a idanuwansu, daga nan kuma sai su ji duk aikin da suka yi ba sa damuwa. Akwai nuni a wasu ruwayoyi da cewa; idan mutum ya rasa kunya ya kasane ba ya jin kunya to yana iya aikata duk wani aiki (na rashin kunya) da ya ga dama. Imam Ali al-Hadi (a.s) yana cewa: “Duk wanda ransa ta wulakanta (a gunsa), to kada ka aminta daga sharrinsa.

Don haka ne nake cewa; ya kai uba mai daraja! ka fitar da danka daga fushin jin haushin kai saboda gudun jin wulakantuwa, ka fitar da shi daga wannan azaba ta ruhi idan ka jefa shi cikinta, sannan kuma tun farko kada ka kai shi ga wannan matsayi domin riga-kafi ya fi magani, ka sani yaran da suka taso suna masu jin izza a cikin ransu, suna masu ganin kima a zukatansu, wadanda suka fito a gidan da suka samu nuni na cikakkiyar soyayya ingantatta kuma sahihiya, to wadannan su ne suke zama masu daukar nauyin gidansu da al’ummarsu a nan gaba, kuma su ne wadanda suke abin dogaro a cikin jama'a.288

[1] Tuhaful Ukul, Ibn Shu'uba Alharrani, Shafi: 483.