Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Mu'assasatu Thaqafatu Thaqlain
Talata

3 Janairu 2017

16:03:00
802504

DARUSSA DAGA RAYUWAR ANNABI MUHAMMAD (SAWA) na 2

Na Maulana Al-Mujahid Sheikh Hamzah Muhammad Lawal(ama) Yusuf Sulaiman ya rubuta maku.

Muka ce an ambaci abubuwa masu yawa wa’yanda babu lokacin yin magana akansu,amma akalla dangane da alakan Manzon Allah (sawa) da Allah Subhanahu wa Ta’ala.Wato a janibin rayuwarshi da yake da dangantaka da ibadunshi.
IBADUN MANZON ALLAH(SAWA)
1.Ya zo daga Al-Imam Al-Husain (as),a wani labari mai tsawo wanda a cikinshi yake fadin yanayoyin  Manzon Allah(sawa).Sai muka dauko wannan.Yana cewa:
“(Manzon Allah) kuma ya kasance yana kuka har ya zama bigiren sallarshi ya jike,saboda tsoron Allah Azza wa Jalla (ba tare da yayi ma Allah Subhanahu wa Ta’ala laifi ba).Saboda gayan tsoron Allah in yana sujada ya kasance ya kan yi kuka har wurin sallan nashi ya jike”.
Wannan akwai shi a cikin Al-Ihtijaj na Al-Dabrasi,shafi 113,
2.Manzon Allah (sawa) ya kasance mai yawan kankan da kai da tawadi’u ya zuwa ga Allah Azza wa Jal,kullum da’iman wa abadan ya kasance yana rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya adanta shi da kyawawan ladubba da kyawawan dabi’u.Saboda haka ya kasance a cikin addu’arshi yana cewa:
  “ ALLAHUMMA HASSIN KHALQI WA KHULUQI”
Ma’ana; Ya Allah ka kyautata halitta ta da dabi’a ta.
Kuma yana cewa : “ ALLAHUMMA JANNIBNIL MUNKARATIL AKHLAQ” Allah ka nisantar dani daga kyamatattun dabi’u.Akhlaq akwai masu kyau akwai marasa kyau.In ka ji an ce maka Akhlaq!dabi’u kenan ake nufi,kaman yanda suka ce akwai FADA’ILUL  AKHLAQ,sannan akwai RAZA’ILUL  AKHLAQ.Wato “Al-Akhlaqul Faadilah” da kuma akasinsu wato “Al-Akhlaqul Raziilah.
Ya kan ce Allah ka nisantar dani daga kyamatattun dabi’u.Wannan akwaishi a cikin Al-Mahasinul Baidah na Al-Faidul Kashani.
3.Ya zo akan cewa kaman yanda a Al-Majma’ul Bayan na Ad-Dabrasi;
Manzon Allah (sawa) ya kasance idan wani al’amari ya tada mashi hankali sai ya nemi mafaka a sallah-“fazi’”a ay “laji’a” an lura.Darasi mai kyau wanda in muka lizimce shi insha Allah zai sa mana sakina da natsuwa da tawakkali da komawa ya zuwa ga Allah Subhanahu wa Ta’ala.
TAWAKKALIN MANZON  ALLAH
Tawakkalin Manzon Allah abin buga misali ne.Da nace tawakkali shima darasi ne daga darussan da zamu koya daga Manzon Allah.
Yana cewa shi da kanshi Manzon Allah(sawa):
  “Duk mutum da ya yanke ya zuwa ga Allah,to Allah zai wadatar dashi,zai isar mashi dukkan bukata-Wannan ba nazariyance za a fahimta ba,a aikace ne,wato shi Tawakkali aikata shi ake yi.Wanda ya yake,ba wai ya iya bayani akan yankewa bane,ana nufin ya yanke akan kanshi ne.Wanda ya yanke ya zuwa ga Allah,to Allah zai wadatar dashi,zai isar mashi dukkan bukata,sannan zai azurtar dashi ta inda ba ya tsammani wato ta inda ba ya lissafi,ta inda ba ya “tawaqqu’i”,ta inda baya jira”.
  “Sannan wanda kuma duk ya yanke ya zuwa ga duniya,to sai Allah Subhanahu wa Ta’ala ya wakkala shi ya zuwa ga ita duniya din,wato sai ya bar shi da ita duniyan har ta koya mashi darasin ta”
Akwai wannan a cikin Jami’us Sa’adat.
Manzon Allah (sawa) yana cewa har yanzu a cikin Jami’us Sa’adat din:
  “Da dai a ce ku kuna dogaro akan Allah Subhanahu wa Ta’ala haqqin dogaro din (ba wai kun iya bayani ba),da an azurtar daku kaman yanda ake azurtar da tsuntsaye”.
Tsuntsaye basu da rumbuna,basu da hisabi(account) a banki,basu da gona da komai amma sai su fita da safe cikunnansu ba komai su dawo sun cika ciki.Suna fita amma basu da komai,kominsu shine wannan fitan da dogaro da Allah Azza wa Jall.
Sannan Manzon Allah(sawa) ya kasance yana cewa kaman yanda yake a cikin Riyadus Salihin na An-Nawawiy Ash-Shafi’I cewa:
  “ALLAHUMMA LAKA ASLAMTU WA BIKA AMANTU WA ILAIKA TAWAKKALTU WA ILAIKA ANABTU WA BIKA KASAMTU.ALLAHUMMA AS’ALU BIKA BI IZZATIKA LA’ILAHA ILLA ANTA AN LA TUDILLANI,ANTA HAYYUL LAZIY TA TAMUT,WAL JINNU WAL INSU YAMUTUN.”In zai fita da safe haka yake fadi.
Ma’ana:Ya Allah ya zuwa gare ka na mika wuya,da kai nayi imani,akanka na dogara,kai nake komawa ya zuwa gare ka,kuma kai nake yin husuma da abokan husuma na,Allah ina rokonka da izzanka,babu ilah in ba in kai ba cewa kar ka batar dani,kai ne mai ran nan da baya mutuwa alhali aljanu da mutane suna mutuwa.
Da darussa masu yawa na na Tawakkalin Manzon Allah (sawa) da kuma alaqanshi tare da Al-Kur’ani da alwalan Manzon Allah (sawa).
Ya zo a taqaice cewa Manzon Allah (sawa) ya kasance ya kanyi alwala domin kowacce sallah(koda yana da alwala,kowace sallah sallah yana jaddada alwala ).To lokacin da shekarar  budi ta zo bayan ya koma Makka wato bayan bude Makka sai ya dinga yin sallah da alwala guda daya (wato yana salloli da yawa da alwala guda daya ).Sai Umar Ibn Kattab yace mashi:Ya Rasulallah ka aikata wani aiki wanda baka kasance kana aikatawa (wato kana yin salloli da alwala guda daya ).
Sai Manzon Allah yace:Da gangan na aikata haka-wato don a san ba wajibi bane,saboda in ba haka ba za a dauka kowace sallah sai anyi alwala.Saboda ruksa sai ya zama nayi haka .
Wannan Al-Muhaddisun Nuriy a cikin Mustadrak alal Wasa’il,da sauransu masu yawa.
Manzo Allah(sawa) daga cikin siffofinshi da dabi’unshi da shaksiyya dinshi akwai riko da “asbab” na yau da kullum wato “asbab ad-dabi’iyya”saboda sanin da yayi akan cewa wannan duniyar duniya ce ta “asbab” da “musabbabat” sabanin “nash’a” din lahira wadda ita dukkan sabubba suna yankewa .Wato “wata qadda’at bihimul asbab.Amma wannan duniyar duniya  ce ta “asbab” saboda haka ya kanyi riko da “asbab”.288