Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkarmusulunci a Nigeria
Talata

15 Nuwamba 2016

16:40:21
792131

Ana ci gaba da Allah waddai kan harin jami'an tsaro kan masu tattakin yankin Kano

Tun daga jiya bayan aukuwan mummunan hare haren jami'an tsaron Nigeria akan masu Tattakin lumana na juyayin Arbaeen da suka taso daga yankin Kano ake ta samun tir da Allah waddai daga kungiyoyi da hukumomin kare hakkin dan adam a ciki da wajen Nigeria. Cikin wadanda suka gabatar da nasu yin Allah waddai.

Akwai al'ummar musulmi mazauna Nairobi na kasar Kenya watau "Mahdi Muslim Community" wadanda suka gabatar da yin tir din su da Allah waddai a rubuce dauke da sa hannun shugaban kungiyar Abdulkadi A Nasser.

Haka nan kuma malamai da masana daga ciki da wajen Nigeria suma sun ci gaba da fitar da bayanai kan wannan mummunan ta'addanci na jami'an tsaron Nigeria akan masu tattakin na lumana daga yankin Kano.

Kamar yadda aka sani har yanzun adadin shahidai na wannan waki'ah nata karuwa saboda wadanda a jima raunuka masu muni da harsasai masu rai na jami'an tsaron.

Wata majiya ta tabbatar da cewa ya zuwa yanzun an tabbatar da shahadar sama da mutane 100.