Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : HAIDAR CENTER ACADEMY
Lahadi

6 Nuwamba 2016

17:46:16
790218

RAYUWAR MA’AURATA KARO NA 4

Na Dr,Hafiz Muhammad Sa'id

WASU DAULOLIN

Al’ummu masu ci gaba da dokoki game da abin da ya shafi mace kamar Kaldaniyawa, Rumawa da Yunaniyawa (Girika) duk ba su tsira daga irin wannan ba, saboda haka zamu yi kokari mu kawo misalai game da matsayin mata a cikin irin wadannan al’ummu.

Kaldaniyawa

A littafin Kaldniyawa na shari’a mai suna “Hamurabi” sun kafa dokar bin mace ga miji da rashin ‘yancinta faufau har ma a cikin nufi, irada, aiki, da bukata. Idan da zata saba masa ko ta yi wani abu na kashin kanta to yana da hakkin fitar da ita daga gidansa ko ya yi mata kishiya ita kuma ya yi mu’amala da ita a matsayin baiwa. Haka ma da zata yi barnar abinci yana iya kaita kotu, idan kotu ta tabbatar da haka to za a nutsar da ita a ruwa har mutuwa[1].

Rumawa

Amma Rumawa suna daga cikin al’ummar da ta dade da kafa dokokin zamantakewa tun shekaru 400 kafin haihuwar Annabi Isa (a.s). A wajansu mai gida shi ne Ubangijin gida da matan zasu bauta masa kamar bayinsa, kuma yana da cikakken zabi, ba ya shawara da mace domin ita ribar kafa ce ta zaman tare kawai da duk abin da ya ga dama shi zai yi, yana iya kashe matarsa da ‘ya’yansa mata idan yana ganin maslahar hakan kuma ba mai ganin ya yi wani laifi, mata, ‘ya, da ‘yar’uwa, duk suna cikin mawuyacin hali.

 Har a Falsafarsu ba a ganin mace wani bangare na al’umma, ba a zartar da cinikinsu ko alkawarinsu, ba su da hakkin zabe ko wasa, amma ‘ya’ya maza koda na tabanni ne suna da daraja domin suna maza. Kuma idan mace ba ta haihuwa miji yana iya kashe ta saboda ba ta kawo ‘ya’ya maza a al’umma, idan namiji ya gane shi ne ba ya haihuwa yana iya bayar da aron matarsa ga wani dan’uwansa idan ta yi ciki ta haihu da namiji sai ya yi alfahari ya samu da.

 Kuma ana iya bayar da rancen mace kamar kaya, sayarwa, bayarwa kyauta, biyan bashi, ko a matsayin haraji, haka nan ba ta tsira daga duka ko kisa ba.

Daga cikin dokokin Rumawa: Mace ba ta dariya, ba zata ci nama ba, ba ta da ikon magana, shi ya sa ma akan sanya mata mukulli a baki, sannan suna ganin ba ta da komai sai hidima ga miji ko ubangida, kuma suna ganin ta a matsayin wasila ce da shedan yake amfani da ita wajan halakar da mutane[2].

Larabawa

Amma Yunan da Yankin Larabawa da Tsohuwar Iran a wajansu gida da maza ne ake lissafinsa ba da mata ba, har ma kusancin da a kansa ake gado[3] da maza ne ake la’akari ba mata ba, babu kusancin da ya shafi mace da ake kiyaye shi koda na uwa ne, ko ‘ya, ko ‘yar’uwa. Kusancin mace da ake kiyaye wa kusanci ne na saduwa, haihuwa, da aurataiya.

A al’adun Larabawa idan ‘ya tana gidan uba ko miji suna iya yin duk abin da suka ga dama da ita, kimar mace hatta ta ranta ba ta da wani alfarma, a sakamakon mace ba ta da wani hakki da ake kiyaye shi sai farkon shahidi a Musulunci ta zama mace. Dukiyar mace ta namiji ce koda kuwa sadakinta ne ko ta kasuwanci da ta yi balle gado da haramun ne a gare ta, uba ko dan’uwa shi ne zai aurar da ita ko ta ki ko ta so.

 Jaririya kuwa ko yarinya ba ta tsira daga binnewa da ranta ba, "Kuma idan wacce aka turbude ta da rai aka tambaye ta. Saboda wane laifi ne aka kashe ta[4]". Suna ganin halittar mace aibi ce da musifa da bala’i gare su[5] musamman ma idan an ribace ta a yaki a wajansu wannan wani aibi ne da babu kamarsa, don haka a binne ta ma da rai don kada ta taso ta zama aibi ga al’ummarsu.

 An ce farkon wadanda suka binne ‘ya mace su ne Banu Tamim sannan sauran larabawa suka dauka, wannan ya kasance ne sakamakon ribace su da sarki Annu’uman dan Munzir ya yi ne[6], sai wannan abu ya fusata su suka fara binne na raye da ransu. Haka nan idan aka yi wa wani albishir da ‘ya mace sai ka ga yana buya daga mutane don kunya na abin aibi da ya samu. "Idan aka yi wa dayansu albishir da mace sai fuskarsa ta zama baka kirin yana mai bakin ciki. Yana mai buye kansa daga mutanen saboda munin abin da aka yi masa albishir da shi, shin zai rike shi ne cikin wulakanci ko kuma zai turbude shi a cikin turbaya ne, hakika abin da suke hukuntawa ya munana"[7]. Amma idan namiji ne aka haifa masa sai ka gan shi yana mai farin ciki komai yawansu, wannan ma ba ya isar sa har sai ya yi da’awar dan zina ma cewa nasa ne, har ma ya kan iya kai wa ga yaki ko fada a kan ‘ya’yan zina[8].

 Koda yake wasu lokuta wasu gidajen sukan ba wa mace damar ta auri wanda take so, ko ma yaya dai, mu’amalarsu da mata mu’amala ce da ta cakuda da ta al’adun daulolin da suke kewaye da kasashen larabawa kamar Iran da Rum.

 A yankin Larabawa mace wata kalma ce ta wulakanci a gaya wa namiji ita kuma kalma ce ta kaskanci. Haka nan mace a wasu al’ummu ta zama murhu ne kawai na dafa abinci ko wanke kaya da yara sai kuma idan bukatar namiji ta taso, amma duk abin da ya shafi ci gaban al’umma wannan wani abin mamaki ne a ga mace a ciki.

Yunan (Girika)

Amma a Yunan[9] al’amarin mata ba shi da bambanci da na Rumawa da suna la’akari da namiji ne a dokokin zamantakewa, komai na namiji ne ba abin da mace take da shi amma a bangaren laifi ana hukunta ta. Haka nan in ta jawo wani abu na amfani to wannan na namiji ne, suna ganin mace kamar kwayoyin cuta ne masu cutar da al’umma, amma ta wani bangare abu ce ta amfanin al’umma, kuma idan ta sake ta yi laifi ko yaya yake, to ta shiga uku.

Mafi yawancin al’ummu ba sa ganin aikinta karbabbe ne a wajan Allah, a Yunan ana cewa da ita dauda daga aikin shaidan, wasu daga Rumawa da wasu Yunanawa suna ganin ba ta da Ruhi irin na namiji. Suna ganin mace kamar wani ribataccen yaki ne da yake kurkuku wanda idan ta kyautata amfani ba nata ba ne, idan kuwa ta munana ta dandani kudarta, kuma ba a gode mata, suna ganin tunaninta sharrin ne kawai, saboda haka ba ta isa a bar ta a kan tunaninta ba.

Haka nan maza su ne kawai al’umma, shi ya sa gidan da babu maza hukuncinsa a rusa shi, don haka idan wani ya ga ba ya haihuwa to dole ya ba da aron matarsa don ta samu namiji, in ba a samu namiji ba sai ya yi tabanni da dan wani ko dan zina ko da kuwa ta hanyar runton da ne da jayaiya. Saki da aure a wajensu iri daya ne da na Rumawa, kuma akan iya auren mata ko nawa aka so amma daya daga ciki ita ce bisa doka sauran kuwa ba bisa doka suke ba[10].

[1]. Almizan, j 2, s: 264.

[2]. Almizan, j 2, s: 265.

[3]. Tafsirin Almizan, Saiyid Diba’diba’I, J 4, shafi 225.

[4]. Surar Takwir: 8 – 9.

[5]. Almizan, j 2, s: 267.

[6]. Abin da ya gabata.

[7]Nahal: 58-59.

[8]. Almizan, j 2, s: 267.

[9]. Almizan, j 2, s: 265.

[10]. Almizan, j 2, s: 266.