Addu’a Domin Fata Nagari Ga Yara
Daya daga cikin muhimman abubuwan da
suka hau kan iya ye shi ne; kiyaye yalwa, da
rabautar yaro a cikin rayuwa, wannan kuwa
yana iya kansancewa ta hanyar yi musu
kyakkyawan fata kodayaushe, da kuma yi
musu addu’a mai kyau, kuma tana daya daga
cikin hanyar arzutarsu ta duniya da lahira.
Sannan kuma mu sani cewa; addu’ar iyaye ga
‘ya’yansu tana daga cikin addu’ar da ba a
mayar da ita.
Don haka ne ma gidan da uwaye suke
tsinewa ‘ya’yansu to tabbas wannan gida
yana tare da lalacewa da tabewa, da kuma
talaucewa da daidaicewa, kuma musifar hakan
ba tana takaituwa, ko tsayuwa kan ‘ya’ya ba
ne kawai, tana shafar har su ma iyaye da suka
yi, don haka ne ma yana daga cikin abu mafi
muni iyaye su rika mummunan fata da
muguwar addu’a kan ‘ya’ya, idan suka yi fushi
da su kada su ce komai idan dai ba zasu fadi
alheri ba, idan kuwa zasu fada; to su ce: Allah
ka shirya mana su.
Don haka ne iyaye ku zage damtse wajen yi
wa ‘ya’yanku addu’a ta gari dare da rana,
- kuma ku ba wa wannan al’amari muhimmanci
na musamman.
Lalacewar mafi yawancin ‘ya’ya sakamakon
mugun baki da la’ana da mummunar addu’ar
iyaye ne, kuma wannan yana shafar har su
iyayen ne, kuma sannan sai ya dame su a
Muna iya ganin wani mutum da ya kai kukan
‘ya’yansa masu tsananin saba masa wajen
manzon rahama (s.a.w), sai Annabi (s.a.w) ya
tambaye shi cewa; Shin ka kyamace su ne (da
mugun baki)? sai ya ce: Haka ne. sai Annabi
(s.a.w) ya ce: Kai ne ka jawo tabewarsu. A
wata ruwayar manzon rahama (s.a.w) yana
cewa: “Ku kiyayi mummunar addu’ar iyaye,
domin tafi takobi kaifi”
Don haka iyaye sai a kiyaye, kuma koda kuna
da hakki kan ‘ya’ya bisa abin da suka saba
muku sai ku kiyaye, balle cewa ma wani lokaci
‘ya’yan ne suke da hakki amma sai iyaye su
runtse idanuwansu, su kawar da kai daga
gaskiya, su yi musu mugun baki!
Mustadarakul wasa'il, Mirza Nuri, j 5, shafi: 256