Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : HAIDAR CENTER ACADEMY
Talata

27 Satumba 2016

17:53:09
781856

LITTAFIN: ALAKAR IYAYE DA ‘YA’YANSU KARO NA 3

BAHASIN: Zabar Suna Mai Kyau

Kamar yadda muka kawo ne cewa akwai tasirin suna maikyau a kan yaro, kuma masu hikima suna ganin cewa; sunan mutum yana nuna al’adun al’ummarsa ne, da addininta, da kuma iyalin gidansu, da akidarsu. Sau da yawa mukan ga mai kyakkyawan suna yana alfahari da shi, kuma yana jin duakaka a kan mai suna maras kyau, kuma wannan yana matukar tasiri sosai a kimar mutum a cikin al’ummar da mutum yake rayuwa. Mun ga irin wannan tasiri sosai ga mai dauke da sunan makasa alayen gidan Annabi gun masoyansu ta yadda ba ya iya fadin sunansa da kyau domin jin kaskanci da kunya,kuma tabbas mutumin da ba shi da sunan da ya dace zai samu jin zogin ruhinsa, da jin wulakantuwa, da kaskantuwa, a cikin al’ummarsa.Imam Bakir (a.s) yana fada game da al’amarin suna mai kyau: “Mafi soyuwar sunaye su ne wadanda suke nuna bauta ga Allah madaukaki, kuma mafi kyawu daga garesu su ne wadanda suke sunaye ne na annabawa1. Sunayen da suke nuna bauta ga Allah (s.w.t) su ne kamar: Abdullah, Abdurrahman da sauransu.Hafiz Muhammad Sa'[email protected] Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)1 Attuhfatus Saniyya, Sayyid Abdullahi Aljaza'iri, sha: 297