Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausa.irib.ir.
Laraba

21 Satumba 2016

09:33:10
780444

Jawabin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Kan Bikin Ranar Ghadir

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa babban sako mafi muhimmanci da Idin Ghadir ke isarwa shi ne nada shugaba a matsayin ginshikin gwamnatin Musulunci.

A jawabinsa ga taron al'umma da suka fito daga sassa daban daban na kasar Iran a bikin ranar Idin Ghadir a jiya Talata: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamene'i ya taya dukkanin al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar bikin Idi Ghadir yana mai fayyace cewa: Hakikanin sakon Ghadir Khum shi ne kafa tushen hukumar Musulunci a duniyar musulmi tare da nuni da cewa addinin Musulunci bai amince da duk wata gwamnatin kama karya ba ko gwamnatin nuna fin karfi ko ta son rai da nuna matsayi ko kuma ta masu girman kai ba, iyaka dai tsarin shugabancin ne da Allah ke nada wanda ya fi cancanta da ake kira da Imamanci a bisa nassi na shari'a.

Har ila yau Jagoran Juyin Juya Halin na Musulunci ya tabo wasu daga cikin dalilan da suke fayyace Imam Ali dan Abi -Talib {a.s} a matsayin wanda ya fi cancantar matsayin khalifancin fiyayyan halitta manzon tsira Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} musamman tsarin shugabancinsa da ya kafu a kan tubalin adalci, shimfida daidaito a tsakanin al'umma, shiryar da al'umma kan tsoron Allah, nisantar duk wani son rai da bata a fagen shugabancin al'umma ballantana kuma uwa uba matsayinsa na farkon wanda ya bada gaskiya da sakon Musulunci tare da sadaukar da kai ga addini, tsarkin zuciya da fifiko kan duk wasu kyawawan dabi'u a bayan manzon Allah {s.a.w}.