Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar Musulunci a Nageria
Lahadi

7 Agusta 2016

14:08:39
770598

Mu ci gaba da kara dunkulewa da magana da murya daya - Malam Yakubu Yahaya

Hirar Wakilin Almizan Aliyu Saleh da Shaikh YakubuYahya don jin matsayar da aka cimma a zaman tattaunawar da aka yi tsakanin bangarorin ’yan uwa daban-daban na Harkar Musulunci a Nigeria a Katsina Ga hirar kamar yadda ya rubuta mana..

ALMIZAN: Mun samu labarin wata ganawa da bangarori daban-daban na Harka suka yi a nan Katsina a karkashin jagorancin Sayyid Badamasi da Sayyid Muhammad bayan ta’aziyyar rashe-rashen da aka yi da suka yi maku. Masu karatunmu za su so jin abubuwan da aka tattauna a wannan zaman?

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Lallai haka ne kamar yadda ka fada, Sayyid Badamasi da Sayyid Muhammad sun jagoranci tawagar ’yan uwa sun kawo ziyarar ta’aziyya na wannan rashe-rashen da muka yi na su Malam Haruna Shelleng da Malam Mika’ilu Abdullahi da kuma shi wannan Yayan namu; Alhaji Sule, wanda sun rasu ne daidai lokaci guda. Ban jima da jin wannan Yayan namu ya rasu ba, sai kuma aka bugu min waya aka fada min wannan mummunan rashin da muka yi. Da taimakon Allah dai aka shanye wannan jarabawar. Muna fatan Allah ya ji kan su da rahama.Bayan ta’aziyyar mun zauna da su, musamman a kan yanayin da muke ci na Harka da kuma irin yadda wasu ’yan uwa ke wasu rubuce-rubuce a Facebook da sauran wurare don kara kwakkwafa tunani a kan abubuwa da dama da kuma halin da muke ciki na waki’a.|angarori da yawa ne suka halarta. Baya ga su Sayyid Badamasi da Sayyid Mahammad, akwai kuma Academic Forum, Mu’assasatu Shuhada, Harisawa, Abul Fadl Abbas, Media Forum, ISMA, Ahlul Duthour, Dandalin Matasa, Lauyoyi da Shu’ara. Almuhim dai abin da ake bukata kowane bangare na Harka ya koma ya yi magana da wadanda suke aiki tare a kan matsayar da aka cimmawa cewa za a ci gaba da ta2ya a kan abin da su Malam suka dora mu a kai.Su Malam sun asassa wannan Harkar a kan bin nizami. Ka san a lokacin da aka yi waki’ar da aka kona gidan Alhaji Hamid Danlami (Allah ya ji kan sa da rahama), su Malam sun yi magana a 2lin idi a cikin jama’a, cewa kar mutane su dauka kamar kara-zube muke, ba ‘crowd’ muke ba, kowa an san daga inda ya zo. Mutum ya san Halkarsu, ya san Wakilin Halkarsu da Majalisinsu, Da’irarsu da kuma Yakinsu (Zones) dinsu. Saboda haka an san kowa. Wannan shi ake ce ma nizami. In mutum yana da wata matsala zai fara ne daga Majalisinsu da kuma Halkarsu. In kuma yana wani bangare ne na Harka, kamar a ce shi dan Academic Forum ne, zai koma wajen Shugaban wannan bangaren. Su ma suna kan tsarin nan da na fada maka, suna ta2ya ne a karkashinsa. Kowane bangare akwai jagorancinsa, kuma in aka dunkule jagorancin gaba daya, za ka ga ya koma abu guda ne, illa dai kawai an raba aiki ne. Kowa da aikin da ya tsayu da shi. Haka muke bukata su ’yan uwa su kasance, musamman a wannan lokaci muwuyaci. Sannan kuma daga cikin manya-manyan nasarorin da za mu iya cewa mun samu a wannan kwarya-kwaryar jalsa shi ne; su Harisawa da ’Yan Abul Fadl Abbas sun kara samun fahimtar juna, domin mun fahimci su’Yan Abul Fadli Abbas din suna kora2n cewa akwai wasu suna yin wasu abubuwan da yawunsu, amma ba da saninsu ba. Amma yanzu tunda ga su ga Harisawa, (muna fatan a shawo kan lamarin). Kuma akwai matsayar da aka yi a lokacin Tattakin nan na bana, wanda suka zauna tsakanin Abul Fadl Abbas din da kuma Harisawa, suka samar da matsaya suka kai wa su Malam, kuma su Malam suka sanya albarka, kuma abin ya yi kyau sosai yabiya bukata, wannan matsayar muke so ya zama ta ci gaba. Haka muke somu ga ana yin aikin tare.Haka kuma mun tsaya a matsayar cewa a ci gaba da abin da ake yi na gayyatar bangarorin Harka idan wani bangare na taro. Kamar idan Harisawa na taro, akwai bukatar su gayyato wasu bangarori na Harka, ko da wakilcinsu su halarta, don su ga me ake yi, don hakan ya zama ya karabunkasa fahimta. Kuma tattaunawa ta gefe duka takan yi fa’aida.Sannan kuma mun cimma matsayar cewa duk wata magana da za ace Harka ta ce, wajibi ne a ji shi daga wajen Malam Ibrahim Musa, Resource Forum, Lauyoyinmu, ko kuma wadanda suka wakilta. Saboda shi Malam Ibrahim shi ke magana da yawun Harka a jaridance, ba wani ne kawai saboda ya iya rubutu, ya iya shiga media, sai ya ce an ce kaza, ko za a yi kaza, ko a zo a yi kaza ba. Idan mutum bai samu Malam Ibrahim Musa ko wanda ya wakilta ba, kuma yana neman karin bayani, to ga Halkarsu nan, ga Da’irarsu nan, ga Majalisunsu nan, ga dai wakilci daban-daban da za a iya yin magana murya daya. Idan ma dan wani Forum ne sai ya koma wa Forum din don ya ji me ake ciki. Wannan shi ne zai taimake mu ya zama aikinmu ya zama bai-daya, kamar yadda su Malam suka dora mu.Ba mu ce ba mu da mishkiloli ba, muna da matsaloli, amma kuma idan aka duba nasarorin da aka samu, sai a ce alhamdullahi, a iya cewa nasarorin sun doke matsallolin. Dama ita matsala babu yadda za a yi ka ce za ka rabu da ita. Idan ka tara mutane dole ka yi hakuri da matsaloli. Idan kana da mutum 10, to kana da matsaloli 10 ke nan. Idan kana da 100, kama da matsaloli 100. Idan kana da 1,000, kana da matsaloli 1,000. Idan ka ce kar a yi matsala, kai ma ka zama matsala. Matsalarka ita ce ba ka bari an yi matsala ba. Shi dan Adam kamar ka ce an kwaba jininsa ne da matsala aka yi shi. A cikin hikimar su Malam, sai suka ce ita matsala bakawar da ita ake yi ba, hakurin zama da ita ake yi, ba maganin matsala ba.Sannan kuma su Malam sun sha fada mana cewa, su da suke tsare ba su ne za su fada mana abin da za mu yi ba. Mune da ke waje za mu ga me ya kamata mu yi? Amma kar mu manta akwai nizamin da ake ta2ya a kai, wanda su Malam suke karfafawa na cewa a lizimci nizamin. Ba yana nu2n in ka ga abu kawai ya dace, sai ka bugi kirji ka je ka yi ba. Duk wani abu da ake yi a Harkar nan an san yadda ake yin sa. Kowane taro da ake yi akwai wadanda ke da mas’uliyar shirya shi. Idan ka je wajen za ka ga kowa da aikin da ya tsayu a kansa. Haka Malam ya koya mana. Kuma har yanzu a haka muke ba a canza ba.Kamar misalin wannan rubutun da Sayyid Muhammad ya yi, wanda ya motsa zukatan masu imani da masu tausayi na duniya, ka ga ba wai yaba da umurnin cewa a yi gangami ko taro ba ne, cewa ya yi ‘in ta kama gaabin da zai yi’. Kuma Alhamdullahi yana wajen wannan zaman da aka yi. Ya sake maimaita wannan maganar cewa shi bai ce a yi gamgani ko Tattaki ba, cewa ya yi in ta kama. Sai ya ce sai a jira ta kama din sannan ayi. Ka ga komai za mu yi muna da tsari da kuma yadda ake yin sa a Harka. Idan za a yi a Harkance ne an san yadda za a yi, amma in wasu mutane biyu ko goma ne suka shirya, aka ce wa ya sa su? Suka ce Sayyid Muhammad ne, ka ga sun yi masa karya. In sun ce Harka ce, sun yi wa Harka karya. In suka ce su suka sanya kansu, ka ga wannan kuma ya sabawa nizamin ita Harka din da abin da su Malam suka dora mu a kai.Idan mutum yana jin shi matashi ne, yana da kar2n hali da imani, na’am imani yana caza mutane, masu wannan yunkuri imani ya sanya su haka da yarda da wulaya, amma kuma kar mu bari wannan ya 2tar da mu daga da’a. Da’a ga su Malam, da’a ne zuwa ga Allah Madaukakin Sarki. SuMalam ba su dora mu a kan komai, sai ga abin da Allah ke so, ba su hana mu sai abin da Allah da Manzo ba su so. Saboda haka tunda sun ce mana ga yadda za a yi nizami ya ta2 daidai, sautinmu ya zama bai-daya, wannan shi ya 2 kusa da mun yi ibada mu samu yardar Allah.A wajen wannan zaman mun tattauna irin matsalolin da aka samu, da kuma nasarori. Daga cikin babbar nasarar da muka samu kasantuwar shi Malam yana raye. Wannan babbar mu’ujiza ce da Allah ya ga dama ya nuna wa duniya.Sannan kuma ita Harkar tana nan ta ci gaba da wanzuwa. Domin su wadanda suka kawo mana hari, sun yi niyyar kashe Malam ne da kuma Harkar, tare da dukkan ’yan uwa gaba daya. Amma sai ya zama su Malam suna nan, Harkar ma haka, kuma tana ci gaba da kara bunkasa. Yanzu Harkar ta zama ta duniya gaba daya, sakamakon harin da aka kawo mana.Ka ga wannan ci gaba ne sosai.Kuma akwai matakai da muke dauka na di9omasiya, na Muzaharori, gangami, magana da ’yan jarida, tuntubar kungiyoyi na ciki da waje, aikin Lauyoyi, shirya taruka kala daban-daban, ciki har da wadanda aka yi a Darur Rahama da kuma Abuja domin tunawa da Shahidanmu na Kudus, dakuma tattaunawar da masana suka yi a kan wannan harin da aka kawo mana da sauransu. Daga nan kuma sai a je mataki na gaba. Shi kuma idan za a dauke shi ba kowa ne zai dauka a kashin kansa ya yi abin da yake so ba, za mu hadu ne mu ga me ya 2 dacewa a yi? Sannan sai a sanar da kowa a Harkance, sai ya zama ya hau kan kowa ya yi. Amma idan ya zama mutum shi zai bugi gaba, ya je ya yi don yana ganin ba a iyaba, ko rauni, ko ba a sauraron umurnin kowa, ko wani abu mai kama da haka, zai zama shi ya bai wa kansa umurni ke nan. Idan mutum 10 ya tara, ya zama umurninsa suke bi ke nan shi ma, shi kuma ya ce ba a bin umurnin kowa.

ALMIZAN: A wannan yanayin, wane abu ke nan ya kamata su ’yan uwa su yi?

SHAKH YUKUBU YAHAYA: Mataki na farko dai mu kara neman kusanci da Allah, mu sani addini muke yi, ba son ranmu ba. Mu ci gaba da kara dunkulewa da magana da murya daya. Kar mu yarda ’yan kwallo su 2 mu hikima. Ka ga team din kwallo mutane 11 ne, kowa da aikin da yake yi. Dazarar wani ya shiga aikin wani, sai ka ga an samu matsala. Imam Ali (AS) ya umurce mu da jin tsoron Allah da kuma nazzama al’amuranmu.

ALMIZAN: Mun gode kwarai.

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Ni ma na gode