Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkarmusulunci a Nigeria
Lahadi

17 Afirilu 2016

17:04:19
748049

Watanni hudu bayan kisan kiyashi a Zaria - Har yanzun muna Neman ayi adalci

Yau watanni hudu ke nan da sojoji suka yi mummunan kisan kiyashi a kan fararen hula, 'yan uwa musulmi na Harka Islamiyya, mabiya Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky a Zariya, jihar Kaduna. Tun bayan aukuwar wannan abin takaicin muke ta shaida wa jama'a gaskiyar al'amuran da suka faru a wadannan kaddararrun,

Yau watanni hudu ke nan da sojoji suka yi mummunan kisan kiyashi a kan fararen hula, 'yan uwa musulmi na Harka Islamiyya, mabiya Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky a Zariya, jihar Kaduna.

Tun bayan aukuwar wannan abin takaicin muke ta shaida wa jama'a gaskiyar al'amuran da suka faru a wadannan kaddararrun kwanaki uku na bakin ciki, daga 12-14 ga Disambar 2015, amma ta yiwu saboda irin munin ketar da sojojin suka yi, jama'a da dama suka kasa yarda da bayananmu. Mun yi ta fadin cewa wadanda aka aika su yi wannan kisan kiyashi, sun yi shi ne kamar ba sojojin kasa, horarru ba, kai ka ce irin kungiyoyin ta'addancin nan masu riyawar jihadi irin su ISIS da ma Boko Haram ne. Sun kashe mata, yara kanana, kona mutane da ransu har mutuwa da kuma amfani da muggan makamai kan fararen hula. Sun kona gidaje, wasu ma da mutane a ciki, kuma suka rugurguza su da motar rusau.

Mun yi ta fadin cewa muna da jerin sunayen mutane kusan dubu da suka bace tun bayan ta'asar da sojoji suka yi a Zariya. Mun ma buga sunayensu don jama'a su gane wa idanunsu. Mun kuma fadi cewa sojoji sun binne 'yan uwa musulmi a katon rami. Amma kamar akasarin jama'a ba su yarda cewa wadannan munanan ta'asoshi za a iya yin su a karkashin gwamnatin da ke ikirarin bin tafarkin dimokradiyya ba, inda bin doka da oda ya kamata ya zama jagaban kowane al'amari. Mun sha nanata wa jama'a cewa abin da ya faru a Zariya fa ba arangama ba ce tsakanin sojoji da 'yan uwa musulmi na Harkar Musulunci, a'a wani shiryayyen tsari ne aka aiwatar da shi don murkushe Harkar Musulunci daga doron kasa da sojoji suka aiwatar. Ai duk wani al'amarin da za a ce an bindige mutane sama da dubu ba tare da asarar ran jami'in soja ko kwara daya ba, bai cancanci a kira shi arangama ba, kawai dai sojoji ne suka kai hari kan 'yan uwa musulmi da ba sa dauke da makamai.

Amma da alama bayanan da suka rika fitowa daga zaman Kwamitin binciken rikicin da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa suna gaskata zantuttukanmu kan kisan kiyashin. Yanzu dai gwamnatin jihar Kaduna ta yi ikirari ta hannun Sakatarenta na gwamnati cewa, ta binne 'yan uwa musulmi 347 a katon rami guda a Mando, Kaduna, da suka hada da mata da yara. Wato gwamnatin jihar Kaduna ta yarda da cewa, da gaske ne sojoji sun kashe mata da yara da ba su rike da makami, kamar yadda muka sha fada a baya. Gwamnatin Kaduna dai, karshe ta aminta cewa sojoji sun kashe daruruwan mutanen da ba su dauke da makami. Mu da ma mun san gaskiya za ta yi halinta komai daren dadewa. Amma a sani cewa abin da gwamnatin jihar Kaduna ta fadi wani dan somin tabi ne na irin mummunan kisan kiyashin da sojoji suka yi a Zariya. Don haka muna bukatar ta dauki alhakin munanan abubuwan da suka faru na bacewar sama da mutane dubu, ta kuma shaida wa duniya inda ta binne su. Ya kamata a ce kawo yanzu jama'a su gaskata bayananmu kan yadda wannan ta'annuti na ban takaici na watan Disambar 2015 a Zariya ya wakana. Gwamnatin jihar Kaduna tare da hadin guiwar sojojin Nijeriya dai sun aikata munanan laifukan yaki ne ta hanyar kashe fararen hula da rusa gine-ginensu da kuma binne su a katon rami.

Ba ma wannan ba kawai, Jagoranmu Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky, matarsa da daruruwan 'yan uwa musulmi har yanzu ana tsare da su ba bisa ka'ida ba. Batun Shaikh Zakzaky da matarsa, Malama Zeenat Ibrahim ya fi muni, saboda su ana tsare da su ne ba tare da wata tuhuma ba, alhali suna tsananin bukatar kulawar Likitoci, wanda mun yi amannar gwamnatin Tarayya ba za ta iya samar da su ba.

Kwanan nan tare da hadin guiwar kungiyar kare hakkin dan Adam na Musulunci da ke London, mun shigar da kara a kotun duniya kan manyan laifuffuka, don ganin mun samu adalci kan wannan batu na laifukan yakin da sojoji suka yi. Ban da wannan ma mun shigar da karar sojoji, DSS da Sufeto-Janar na 'yan sanda a babbar kotun Abuja muna neman a tabbatar da hakkin dan Adam na Jagoranmu, Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa, Malama Zeenat Ibrahim.

Kuma a yayin da muke wannan fitowar ta lumana, muna neman a sake su ba tare da wani sharadi ba, muna kira ga duk wani mai yi wa kasar nan fata na gari, ba tare da nuna bambancin addini, kabila da yanki ba da ya hada hannu da mu don ganin an yi adalci a kan kisan kiyashin Zariya, wadanda kuma suka yi shin an zartar musu da hukunci. Abin da ya faru a Zariya a watan Disamba wani al'amari ne da wasu sojoji masu zubar da jinin mutane suka aiwatar kan fararen hula. Idan ba ka damu da hakan ba, to wata ran abin na iya fadowa kanka ta hannunwadannan sojoji 'yan ina-da-kisa. Kar mu yi shiru, mu yi magana kan rashin adalcin da aka nuna wa 'yan uwa musulmi na Harkar Musulunci a Zariya.
Aminci ya tabbata ga masu bin shiriya
Abdulhamid Bello
15/04/16