Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkarmusulunci a Nigeria
Asabar

12 Maris 2016

16:38:34
740571

Yadda aka yi gangamin kiran # A saki Sheikh El-Zakzaky a garin Ilorin, jihar Kwara

An ci gba da gudanar da gangami da muzaharori a birane daban daban a fadin Nigeria har da kasashen ketare, na yin kira da a gaggauta sakin jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da sauran dukkkanin wadanda suke tsare a gidajen kaso daban daban a fadin Nigeria.

Mahalarta wadannan gangami da muzaharar sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna kira a gaggauta sakin sa tare da dukkanin wadanda suke tsare.

Tun bayan hare-haren ta'addancin da sojojin Nigeria suka kaiwa Harkar Musulunci a Nigeria, da kutsen da suka yi a gidan jagoran Harkar a Gyallesu ake ta gabatar da gangami da muzaharori a baki dayan kasar ana kiran a gaggauta sakin Sheikh El-Zakzaky.288