Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nageria
Talata

8 Maris 2016

10:30:46
739672

Hukumar binciken kisan da sojoji suka yi a Zariya ta sake dage zamanta karo na uku

Ta dage zaman ne a yau zuwa wata ranar Litinin mai zuwa. Dalili shi ne Lauyoyin Harkar Musulunci ba su gana da Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ba. Lauyan Hukumar ya nemi a ci gaba da zama, amma Ciyaman na Hukumar ya ce a'a. Don haka ya umurci Lauyan Hukumar ya zauna da Antoni-janar na jihar Kaduna.

HUKUMAR BINCIKEN KISAN KIYASHIN DA SOJOJI SUKA YI A ZARIYA TA SAKE DAGE ZAMANTA A KARO NA UKU

Ta dage zaman ne a yau zuwa wata ranar Litinin mai zuwa.
Dalili shi ne Lauyoyin Harkar Musulunci ba su gana da Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ba.

Lauyan Hukumar ya nemi a ci gaba da zama, amma Ciyaman na Hukumar ya ce a'a. Don haka ya umurci Lauyan Hukumar ya zauna da Antoni-janar na jihar Kaduna da Lauyoyin Harkar Musulunci, lalle a je a ga Jagora kafin ranar Litinin 14 ga Maris, 2016.

Wai tsoron me jami'an tsaro suke ji ne da ya sa sati uku ana abu daya, wato yunkurin ganin Jagora Shaikh Zakzaky?
Rana dai ba ta karya, sai dai uwar diya ta ji kunya. Allah ya kaimu Litinin din mai zuwa.